Cikin shirin za a ji yadda majalisar dattawan Amirka ta sake wanke tsohon Shugaba Donald Trump. Yayin da ake ranar masoya ta duniya, wasu kurame a Najeriya sun damu da yanda sauran al'uma ke kin kula su a harkar soyayyar. A Kamru kuwa an cika shekara guda da kisan wasu kananan yara da sojojin kasar suka yi.