A cikin shirin za a ji cewa Gwamnatin Najeriya ta bayyana matakin dage takunkumin da ta sanyawa wasu kungiyoyin agaji a yankin Arewa maso gabashin Najeriya bayan zarginsu da taimakawa ta'addanci, a yayin da a Jamhuriyar Nijar hauhauwar farashin kayan abinci ne ke cigaba da jan hankalin al'umma.