A cikin shirin za a ji cewa, a Najeriya, gwamnatin jihar Yobe ta fito fili ta bayyana wa 'iyayen 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da aka sace cewar ba a kubutar da su ba, batun da ke cin karo da juna tun bayan da 'yan Boko Haram suka yi awon gaba da 'yan matan.