A cikin shirin za ku ji cewa Makonni bayan shan rantsuwar kama aiki, Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sunayen mutanen da yake son nadawa a matsayin ministoci ga majalisar dattawan kasar don tantancesu, sai dai yanayin mutane da shugaban ya zaba da ma adadinsu yayi hannun riga da ikrarin da ya rinka fadi a yayin yakin kin neman zabe akwai sharhi na musamman da DW ta rubuta kan wannan batu.