1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da harin 7 ga watan Oktober a Isra'ila

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2024

Harin ta'addancin da Hamas ta kai wa Isara'ila wanda daga bisani ya jawo yakin Gaza- ya haifar da sauyi a wasu kasashen Larabawa, Babban da suka hada da Saudiyy, Lebanon, Siriya da Masar dama yankin yammacin Jordan

https://p.dw.com/p/4lQpx
Zanga zangar 'yan Israila ta bukatar musayar fursunoni
Zanga zangar 'yan Israila ta bukatar musayar fursunoniHoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu/picture alliance

Idan muka faro da kasar Saudi Arabiya yadda matsayinta ya yi ta sauyawa tun daga ranar 7 ga Oktoba. Inda na farko Saudiyya ta rufe duk wata tattaunawar hulda da Isra'ila inda maimakon hakan Saudiyya a yanzu ta mayar da matsayinta na mai amfana da batun tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin Hamas da Isra'ila. Sebastian Sons babban mai bincike ne na tsarin al'amuran Jamus.

"Tun 7 ga watan Oktoba, Saudiya ta samu kanta cikin wani yanayi na tsaka mai yuwa inda ta ke yin taka tsantsan kan tsaron cikin gidanta tun bayan da al'umara su ka kara dagulewa a yankin. A gefe guda kuma masarautar ta Saudi na nuna Kanta a matsayin wace ke da alhakin kare bukatun Falastinawa, yayin da a daya bangaren batun maida huldarta da Isra'ila ta ke son jinginewa a aiwatar da shi daga baya. Don haka Saudiyya na daidaita Lamarin wato a fili ta fito da kakkausar sukar matakin sojan Isra'ila, a daya bangaren kuma kuma tana kokarin ganin warware rikicin ta difalmasiyya”

Karin Bayani: Sojojin Isra'ila sun kutsa Zirin Gaza ta kasa

Harin Hamas a Isra'ila a lokacin bikin al'ada
Harin Hamas a Isra'ila a lokacin bikin al'ada Hoto: Alexi J. Rosenfeld/Getty Images

Kasar Lebanon ana batun yakin Gaza, kuma babu kasar da hakan ya jikkata kamarta, musamman kasancewar Lebanon dama can talauci da rashin mulki mai dorewa ya kusan kassarata tun gabanin barkewar yakin na Gaza. Ga kuma Hizbullah wace ta tsudduma kanta cikin yakin da Isra'ila ke yi da Hamas. Kelly Petillo, kwararriya ce kan yankin Gabas ta Tsakiya a hukumar Tarayyar Turai.

" Tun gabanin harin watan Oktoba, Hizbullah ta yi ta hana gudanar da zaben shugaban kasar Lebanon, abinda kuma za a ce ya kara taimakawa wajen hana zaben shi ne matsin lamba sai an gudanar da binciken abinda ya haddasa mummunan fashewa a birnin Bairut, inda babu ko mutum guda da aka hukunta bisa aikata laifin.”

Karin Bayani: Duniya na Allah wadai da sabon rikicin Hamas da Isra'ila

Zanga zangar 'yan Isra'ila ta neman musayar fursunoni
Zanga zangar 'yan Isra'ila ta neman musayar fursunoniHoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu/picture alliance

Sai dai kwararriyar ta ce amma kuma Hizboullah ta samu karin karbuwa matuka a wajen ‘yan lebanon musamman wadanda ke jin takaicin abin da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu. Idan kuma aka dubi kasar Jodan ita ma wannan shekarar ta zame mata mai matukar wuya a tarihinta. Yayin da a baya ta ke cin gajiyar gogayyarta da Isra'ila, amma yanzu ta samu kanta cikin gaba kura baya siyaki, domin in ta juya wa Falastinawa baya to boren ‘yan kasar dama ya kai iya wuya, haka kuma in ta ki bin muradun Isra'ila to tsaronta da sauran yajeniyoyi za su rushe a cewar Kelly Petillo,.

Zanga zangar kawo karshen yakin Gaza
Zanga zangar kawo karshen yakin GazaHoto: Ammar Awad/REUTERS

"Batun huldodidinsu da Isra'ila masu muhimmanci kamar na tsaro da ruwa suna cikin barazanar rushewa. Ka san cewa tun fara yakin Jordan na kokarin daidaita karfin goyon baya ga al'ummar Falastinu tare da alakar ta da Isra'ila”

Sai dai ga kasashen Siriya da Masar ana iya cewa yakin riba ya zame musu, misali Siriya shugaba Assad ya mayar da hankali wajen sake shiryawa da kasar Turkiya da kasashen Tarayyar Turai kuma yana samun nasara, yayin da sauran kasashen da suka shiga Siriya da sunan yaki da ta'addanci suna kara raba kan 'yan Siriyar suna ta kwasar azikin kasar hankali kwance domin idan ana batun Gaza ba a duba me suke diba na arzikin Siriya. Ita kuwa Masar da ta kasance babbar mai shiga tsakani kuma mai iyaka da Gaza har ta samu tukwicin dala biliyan daya da miliyan dari uku a bara na taimakon aikin soja.