1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi amai ta lashe kan kulle

Jens Thurau ZMA/LMJ
March 25, 2021

An shirya tsananta dokar kulle ta tsawon kwanaki biyar lokacin bukukuwan Easter a Jamus. Kwana biyu bayan nan, shugabar gwamnati Angela Merkel ta nemi afuwa tare da janye batun.

https://p.dw.com/p/3r8i5
Deutschland | Bundestag | Angela Merkel gibt Regierungserklärung ab
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na fuskantar kalubale kan dokokin coronaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Karshen watan Maris na 2021, na zuwa ne cikin wani yanayi da ke nunar da cewar gwamnatin Tarayyar Jamus na cikin tsaka mai wuya game da yaki da annobar corona. Hakan ya sanya dasa ayar tambayar da a baya babu wanda yayi tunaninta: Shin Angela Merkel za ta iya cimma tsari mai ma'ana da zai yaki wannan annoba? Ko kuma za ta yi murabus daga mukamin shugabar gwamnati? Cikin sharhin ya rubuta Jens Thurau na tashar DW ya nunar da cewa, ba za a kai ga wannan matakin ba tunda babu wanda yake son karbar ragamar shugabanci cikin mawuyacin yanayin da kasar da ta dauki gomman shekaru ba ta gani ba.

Karin Bayani: Abubuwan da za a tunkara a 2021 a Jamus

Sai dai sannu a hankali karfin ikon wannan jarumar shugaba da duk duniya ke alfahari da ita tare da ba ta daraja, ya fara raguwa a cikin gida. A farkon wannan makon ne dai a taronta da gwamnonin jihohin tarayya, a yanayin ta na jajircewa Angela Merkel ta nemi tsawaita dokar kullen kasar da makonni hudu, a tsakiyar taron ne aka ayyana matakin rufe dukkan wurare a lokacin bukukuwan Easter. Matakin na tsayar da komai har tsawon kwanaki biyar ya jefa mutane cikin tunanin dalilin hakan, ganin cewar babu wanda ke muradin yin bulaguro duba da halin da ake ciki.

Kuna sha'awar samun karin bayani kan halin da ake ciki a ko da yaushe kan coronavirus? Jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amirka, ta samar da taswira kamar yadda za ku iya gani a nan:

Sai dai wasu na muradin su dan zagaya a lokacin hutun na Easter, batun da ya janyo barazanar yin watsi da sauran yarjejeniyoyin da taron ya cimma a bangaren shugabar gwamnatin. Wannan barazanar ba ta wuce sa'o'i ba, zanga-zangar adawa ta barke  bdaga 'yan kasuwa da Majami'u da ma 'yan adawa. A fili ministan cikin gida Horst Seehofer na jam'iyyar CSU, ya nuna adawarsa kan dokar kullen ta kwanaki biyar. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tasirin jam'iyyar Merkel ta CDU ke kara lalacewa a zabukan baya-bayan nan, wanda ake alakantawa da yadda manyan 'yan siyasar jam'iyyar ke azurta kansu daga badakalar sayen takunkumin kariya daga corona.

Karin Bayani: Taron G20 ya kuduri aniyar kawo karshen corona

To sai dai daga bisani, Merkel ta fito fili ba wai kawai ta janye kalaman nata a matsayin kuskure ba, amma ta nemi afuwa daga al'ummar kasar baki daya a gaban majalisar wakilai ta Bundestag. Ba kasafai ake jin irin wadannan kalamai na neman afuwa a wajen shugabannin gwamnati musamman a bakin mutane masu kima a idon duniya kamar Angela Merkel ba.

Kommentatorenfoto Jens Thurau
Jens Thurau na tashar DWHoto: DW

Bisa dukkan alama dai, babu cikakkun bayanai daga bangaren gwamnati da ma kasar. Illar hakan kuwa shi ne, al'umma za ta rasa dokar da ya dace ta daraja. Da farko dai dokar hana tafiya, sa'annan aka janye ta. Da yake Merkel na tuntubar gwamnonin jihohin kasar, bayanai na fitowa daga kafofin yada labarai akai- akai, kuma tauraron Merkel na kara dusashewa. Tun bayan barkewar annobar corona, Angela Merkel ta fuskanci kalubalen da ke tattare da cutar fiye da saura. Bayan shekara guda, matakin da ake dauka shi ne kara tsananta dokar kulle. Fara sassauta wannan dokar da gwaji akai-akai, bai haifar da sakamakon da ake muradi ba. Baya ga haka, batun allurar riga-kafi na tafiyar hawainiya. Abin da ke nunar da cewar, Jamus ta rasa alkibla a yaki da annobar corona musamman a yanzu da ake samun karuwar masu kamuwa da ita a kowace rana.