1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kalubalen yaki da coronavirus

October 15, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da gwamnonin jihohi 16 da ke fadin kasar, sun cimma matsaya dangane da tsananta dokokin yaki da cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3jywM
Corona-Gipfel  I  Merkel und Ministerpräsidenten
Taro kan coronavirus a Jamus, ya amince da daukar matakai domin dakile yaduwar cutarHoto: Hayoung Jeon/Getty Images

Matakan dai sun hadar da sanya takunkumi da bayar da tazara tsakanin mutane da kuma rufe wuraren shan barasa da wuri a yankunan da cutar ta fi kamari. Har kawo  yanzu Tarayyar Jamus ta kasance zakaran gwajin dafi wajen yaki da annobar COVID-19, idan aka kwatanta ta da sauran takwarorinta da ke fama da ta'azzarar wannan cuta tun bayan barkewarta, da kuma sake dawowa a karo na biyu.

 A yayin taron da suka gudanar a ranar Laraba dai, shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta jaddada bukatar ci gaba da matsa kaimi wajen yakar cutar ba tare da yin kasa a gwiwa ba, ganin kasar na fuskantar barazana: "Ina da yakinin cewar matakan da zamu dauka da kuma kin dauka a cikin kwanaki da makonni masu gabatowa za su kasance masu tsananin gaske wajen kalubalasntar wannan annoba. Saboda muna ganin yadda ake kara samun hauhawar wadanda ke mauwa da ita. Wasu yankuna da sauki, a yayin da lamarin yake kara kamari a wasu yankuna Jamus."

Kuna sha'awar samun karin bayani kan halin da ake ciki a ko da yaushe kan coronavirus? Jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amirka, ta samar da taswira kamar yadda za ku iya gani a nan: 

Tsananta matakan yaki da corono musamman a yankunan da ake cigaba da samun karuwar yawan wadanda suka kamu da ita, zai dora a kan nasarorin da kasar ta cimma a wannan bangare, a cewar fraministan jihar Bavaria Markus Soeder: "Ko shakka babu ana iya cewa wannan zaman ya samar da ci gaba ga kasar baki daya. Sai dai har yanzu ba mu san ko matakan sun wadatar ba. A ra'ayina har yanzu babu masani dangane da hakan. Idan muka duba halin da ake ciki sa'annan muka yi la'akari da bayanan kwararru a kan wannan batu, ina ganin lokaci ya yi da zamu farka daga barci, mu dauki matakan da suka dace."

Karin Bayani: Za a sassauta dokar zaman gida a Jamus

A karkashin yarjejeniyar dai akwai tsananta matakan fitar dare, musamman a wuraren shan barasa da takaita haduwar mutane da yawa, da ake ganin zai takaita yawan masu kamuwa da cutar zuwa 35 daga cikin dubu 100 idan aka kwatanta da 50 daga cikin dubu 100, nan da  kwanaki bakwai masu gabatowa.

Symbolbild Hände mit Getränken,
Takaita taruwa a wuraren shan barasa a Jamus Hoto: Colourbox

Idan har wadannan mataki suka gaza rage yawan masu kamuwa da coronar, wajibi ne a kara daukar wasu mataki masu tsauri, domin kaucewa dokar zaman gida ko kuma rufe kasar wato  lockdaown a karo na biyu, saboda mummunar illar da hakan ya yi ga tattalin arzikin kasar. To sai dai tuni dokar takaita fitar dare a wuraren shakatawa da cin abinci da ta fara aiki a wasu birane da coronavirus din ta yi kamari ciki har da Frankfurtz, ta fara kassara harkokin kasuwanci.

A karkashin sabuwar dokar dai wajibi ne wuraren cin abinci da shakatawa su rufe da misalin karfe 11 na dare, tare da haramta taron shan barasa a wuraren jama'a da a kan tituna, kuma dole a sanya takunkumi a duk tituna da wurarn cunkoson.

Karin Bayani: COVID-19: Merkel ta ce a yi taka tsan-tsan

Biranen Jamus da dama sun tsinci kansu cikin wani yanayi na karuwar masu kamuwa da COVID-19 cikin makonnin baya-bayan nan. Biranen da ke cikin wannan barazana sun hadar da Cologne da Dusseldorf da Frankfurt da Stuttgart da kuma Munich.