1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Matsalar shaidar karya

October 10, 2023

Al'umma na ganin bayar da shaida na kawo karshen husuma ko kuma hana wata fitina a tsakanin jama'a, irin wannan shaidar ta taka rawa matuka wajen samun nasarori da kuma farantawa wasu marasa karfi.

https://p.dw.com/p/4XLVs
Amtsgericht und Landgericht Hanau
Tsarin shariaHoto: Michael Schick/imago images

Kwatsam sai wannan tafiya ta bayar da sahihiyar shaida ta fara samun nakasu lokacin da son abin duniya da son rai ya fara yi wa mutane yawa, inda yanzu haka shaidar ta sauya salo zuwa ta Zur! inda za ka iske wasu mutane sun mai da yin shaidar zur a matsayin abin neman kudi, in har za ka biya su to fa babu ruwansu a shirye suke su daura alwala kuma su rantse da alkur'ani.

Ba ka ji ba, kuma ba ka gani ba, amma ka ce haka ne, shaidar "zur" ke nan, wato mutum ya tsayu kan ba da shaidar karya bisa abin da ba shi da masaniya,  Ko kuma abin da ya tabbatar da cewa karyar ne, ya zo yana ba da shaidar karya  akai domin a dannewa wani haƙƙinsa ko a cuce shi,

Wasu da dama ba su san mai ya faru ba, kawai  sai ka ga sun zo sai rantse-rantse suke kan abin da ba su gani ba, wai dan gudun kar su ji kunya, ko kuma su goyawa abokansu baya ba, alhali sun san su ne ba su da gaskiya. Wannan shaidar a yanzu haka ta watsu ba ga  maza ba, balle mata. Yanayin da ya sa ababe da dama ke faruwa a wurare dabam-dabam da al’umma ke gudanar da harkokinsu.

Wasu na ganin son abin duniya ke jawo aikata wannan hali, a gefe guda wasu na ganin son rai ne kawai. Haka zalika shaidar karyar ta samu gurbin zama a wuraren sasanci da kuma hukunci, inda abin ya zama kasuwanci musamman ma a kotuna. Yawa-yawan wadanda ake yi wa shaidar zur kan dade da mikin a zukatansu duba da halin da aka jefa su a ciki na kwace abin da suka mallaka ko kuma tura su gidan-kaso.