1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar za ta samu tallafi daga Jamus

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 24, 2022

Jamus ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa Jamhuriyar Nijar a fannin horan sojoji dabarun yaki da ta'addanci da ilimin 'ya'ya mata da kuma yaki da sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/4Bkzt
Yamai, Nijar | Shugaban Gwamnatin Jamus I Olaf Scholz I Mohamed Bazoum
Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar da shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ne ya sanar da hakan Yamai fadar gwamnatin Nijar din, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa Shugaba Mohamed Bazoum. Shugaban gwamnatin Jamus din dai, ya isa Nijar ne a ci gaba da ziyarar da yake a wasu kasashen Afirka uku da suka hadar da Senegal da Nijar din da kuma Afirka ta Kudu.

Karin Bayani: Dumamar yanayi na kara matsalar yunwa a Nijar

Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar din ne dai ne dai ya mika kokon barar kasarsa ga shugaban gwamnatin ta Jamus kan bukatar tsawaita zaman sojojin Jamus na rundunar Gazelle masu aikin bai wa sojojin bataliya ta 41 na  Nijar din da ke garin na Tillia  horo kan dabarun yaki da ta'addanci. Shugaba Bazoum din dai, ya yaba da irin rawar da suka taka ya zuwa yanzu.

Tillia, Nijar | Shugaban Gwamnatin Jamus I Olaf Scholz
Scholz ya ziyarci sojojin Jamus da ke Jamhuriyar NijarHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Da yake amsa wannan bukata ta Nijar, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce tuni majalisar dokokin kasarsa ta amince da wannan bukata: "Rundunar sojojinmu da ake wa lakabi da Gazelle na aiki kafada da kafada da sojojin Nijar. Idanuna sun gane min irin nasarar da wannan runduna ta samu wajen tafiyar da aikinta, abun da ya yi saura a yanzu shi ne mu zauna mu ga yadda ya kamata huldar ta gudana da aikin da ake bukata rundunar ta mayar da hankali a kai a yanzu. Za mu ci gaba da tattaunawa. Nasarar da aka samu a cikin shirin ta sa muka amince da kara wa'adin aikin sojojinmu a Nijar."

Karin Bayani: Ziyarar ministar Jamus a Afirka

Shugaban gwamnatin Jamus din ya kuma bayyana bukatar ci gaba da tallafawa kasashen yankin Sahel, a yakin da suke da ta'addanci. Shugaba Bazoum na Nijar dai, ya kuma bukaci shugaban gwamnatin Jamus da ya taimaki kasarsa a fannin bunkasa karatun 'ya'ya mata domin da magance matsalar auren wuri wacce ita ce ke haddasa karuwar al'umma da Nijar ke fuskanta da kuma ke tauye kokarin da kasar take a fannin tattalin arziki da neman fita daga kangin talauci.