1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke tsarin sakandare a Najeriya

February 7, 2025

Bayan share sama da shekaru 50 bisa tsohon tsari, gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin kawo sauyi bisa tsarin ilimi a kasar tare da soke tsarin sakandare da ke da tsohon tarihi.

https://p.dw.com/p/4qBWe
Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba

Maimakon  shekaru guda shida a matakan firamare da wasu guda uku a karama da kuma babbar sakandare dai, Najeriya na shiri na karkata zuwa wasu shekaru har 12 ba hutu.

Kafin kuma su kama hanyar kai wa ga jami'a cikin tsarin 12-4 da gwamnatin kasar ta kai ga sanarwa.

Nigeria l Schulstart - Schuleröffnung
Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba

Tsarin kuma da Abujar ke da babban fata zai rage yawan yaran da ba su da damar ilimi cikin kasar. Ya zuwa karshen shekarar da ta shude dai Najeriyar ce take sahun gaba cikin batu na yawan yaran da ba sa cikin aji a duniya   baki daya.

To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai sabon tsarin ke fuskantar turjiya ta kwarrarun da ke masa kallon da biyu. A shekara ta 1976 ne dai tarayyar najeriyar ta fara aikida tsarin da Abujar ke neman sauyawa yanzu.

BG 50-jährige nigerianische Schülerin
Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

To sai dai kuma shekaru 50 bayan nan yara kusan miliyan 18 ne ke gararramba a gari sakamakon gaza samun damar ilimin a cikin tarayyar Najeriyar, a fadar hukumar yara ta Majalisar Dinke Duniya UNICEF.

Nigeria Lehrerin in Muslimischer Mädchenschule
Hoto: Hannibal Hanschke/dpa/picture alliance

Soke tsarin yanzun dai na nufin kai karshen  kanana da ma manyan makarantun sakandare a kasar, abun kuma da ke iya hargitsa tsarin ilimin da kila ma shafar makomar dubbai na malaman da ke sana'ar koyarwa a kasar.