1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon rikicin siyasa a Rivers

Muhammad Bello LM
October 3, 2024

Rikicin siyasar jihar Rivers da ke yankin Niger Delta a Najeriya, ya farfado sakamakon zaben kananan hukumomin da ba su dade da samu'yancin cin gashin kai daga jihohi ba a kasar.

https://p.dw.com/p/4lNMG
Najeriya I Ezenwo Nyesom Wike | Rivers | Rikici | Siyasa | Gwamna | Siminalayi Fubara
Tsohon gwamnan jihar Rivers kana ministan Abuja a Najeriya, Ezenwo Nyesom WikeHoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Jihohi da dama dai a Najeriya na ta ruguguwar ganin sun gudanar da zabukan kananan hukumomi, musamman saboda 'yancin cin gashin kai da hukuncin sharia ya ba su a baya-bayan nan. Hukuncin dai ya nunar da cewa ko kwabo ba zai sake shiga aljihun kananan hukumomin ba, har sai an samu zababbun shugabanni ta hanyar gudanar da zaben. Jihar Rivers, ta bi sawun takwarorinta wajen gaggauta zaben kananan hukumomin. Sai dai ganin zaben na shirin tona asirin karfin 'yan siyasar jihar, sabon rikici ya barke. Gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya janye 'yan takararsa zuwa sabuwar jamiyya APP, domin shiga zaben duk da kasancewarsa dan jamiyyar PDP. Matakin nasa dai, ba ya rasa nasaba da kankanewar da tsohon gwamnan jihar kana tsohon uban gidansa wato Nyesom Wike ya yi a PDP din. Ana tsaka da wannan rikicin ne kuma, wata kotu ta umarci dakatar da zaben na Asabar din da ke tafe kana 'yan jamiyyar APC masu mubayi'a ga Wike ke zanga-zangar ganin ba a yi zaben da suka ce za a yi musu wa-kaci-ka-tashi ba.

Najeriya I Ezenwo Nyesom Wike | Rivers | Rikici | Siyasa | Gwamna | Siminalayi Fubara
An jibge jami'an tsaro, domin shirin ko-ta-kwana a jihar Rivers ta NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/U. Ekpei

Koda yake a nasa bangaren, Gwamna Fubara ya ce ba gudu ba ja da baya a wannan zabe. A hannu guda kuma, Hukumar Zabe ta Kasa INEC da aka zarga da hana yin rijistar masu zabe a jihar, ta bayyana cewar ba ta da hannu a zaben kananan hukumomi har yanzu. An jibge jami'an tsaron rike da makamai suna gadin mashigar Hukumar Zaben Jihar RSIEC, inda ake zargin hakan wata niyya ce ta hana duk wani abu da ke da nasaba da zaben. Sai dai a jawabin rundunar 'yan sandan jihar ta gabatar kan batun zaben, ta ce kokari ne na hana wasu kai farmaki kan gine-ginen hukumar. Nathaniel Akpos, shi ne shugaban kungiyoyin sa ido kan wannan zabe na kananan hukumomin jahar ta Rivers. Wani babban batu dai mai daure kai shi ne yadda kwatsam aka sanar da dauke kwamishinan 'yan sandan jihar tare da kawo wani sabo. Ko da ya ke dai sauran jam'iyyun da suka hada da wani bangaren jam'iyyar APC da Rotimi Amaechi ke jagoranta, sun bayyana shirinsu na shiga zaben. Gwamna Fubara ya ja kunne na jifa a kasuwa, inda ya ce Hukumar Zaben ta jiharsa ba ta kowa ba ce ta al'ummar Rivers ce kuma wani ko wasu da ke da jimirin kawo cikas a wannan zabe za su sha mamaki.