1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Mark Rutte sabon sakataren kungiyar NATO

Bernd Riegert SB
October 1, 2024

Mark Rutte tsohon firaministan Netherlands ya zama sabon sakataren kungiyar tsaron NATO inda ya karba daga hannun Jens Stoltenberg. Rutte zama mai tasiri tsakanin kasashen duniya saboda karfin kungiyar da yake jagoranci.

https://p.dw.com/p/4lIg9
Beljiyam Brüssel | NATO/OTAN | Mark Rutte
Mark Rutte sabon sakataren kungiyar tsaron NATOHoto: John Thys/AFP

A wannan Talata da ke zama daya ga watan Oktoba, tsohon firaministan Netherlands ya fara aiki a matsayin sabon shugaban kungiyar tsaron NATO/OTAN, abin da zai tantance kwarewarsa kan harkokin diflomasiyya. Haka na zuwa lokacin da kungiyar take bai wa Ukraine goyon baya sakamakon kutsen da ta take fuskanta daga dakarun Rasha.

Karin Bayani: NATO da Ukraine na yin taro

A watan Yulin shekara ta 2023 Mark Rutte ya bayyana cewa zai ajiye aiki a matsayin firaministan Netherlands tare da fita daga harkokin siyasa bayan gwamnatin da yake jagoranta ta rushe sakamakon manufofin da suka shafi masu neman mafana. Zuwa watan Oktoba na shekarar Rutte ya manta da duk alkawuran da ya yi, inda ya nuna sha'awar jagoranci kungiyar tsaron NATO/OTAN, domin maye gurbin Sakatare Janar na kungiyar Jens Stoltenberg wanda ya bayyana yin ban kwana da mukamun daga kasrhen watan jiya Satumba na shekara ta 2024, bayan shafe shekaru 10 yana jagorancin kawancen.

Beljiyam, Brüssel | Amtsübernahme als NATO Generalsekretär durch Mark Rutte
Mark Rutte sabon sakataren kungiyar tsaron NATO da Jens Stoltenberg wanda ya sauka daga mukamunHoto: Yves Herman/REUTERS

Sabon Sakatare Janar na kungiyar tsaron ta NATO, Mark Rutte ya shafe tsawon shekaru 14 a matsayin firaministan Netherlands, kuma  yanzu yana da aikin tabbatar da kungiyar ta ci gaba da tafiya a matsayin "tsintsiya madaurin-ki daya" inda akwai masu siyasar kishin kasa a kungiyar irin Firaminista Viktor Orban na kasar Hangari, duk da yake shi kansa Rutte yana iya shawo kan masu ra'ayin mazan jiya a siyasar Turai. Shi dai Orban ya kasance mai dasawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Rutte ya dade yana sukar manufar Shugaba Vladimir Putin na Rasha musamman saboda kakkabo jirgin saman saman fasinja a gabashin Ukraine a shekara ta 2014, inda kusan mutane 300 suka halaka galibi 'yan kasar Netherlands, wadanda suke cikin jirgin saman na Malesiya da ya tashi daga birnin Amsterdam na Netherlands zuwa Kuala Lumpur babban birnin kasar Malesiya. Kuma masu bincike na kasashen duniya sun tabbatar da cewa an yi amfani da makamun roka na Rasha da 'yan awaren gabashin Ukraine suka harba.