1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Kungiyar tsaro ta NATO da Ukraine za su gudanar da taro

Abdourahamane Hassane
August 28, 2024

Kungiyar tsaro tra NATO da Ukraine za su gudanar da taro, bisa bukatar hukumomin Kyiv, bayan da Rasha ta kai hare-hare a kan biranen Ukraine da yawa inda ta haddasa mumunar barna.

https://p.dw.com/p/4k0q4
Hoto: Valentyn Ogirenko/REUTERS

Ministan tsaronUkraine  Roustem Oumerov zai yi magana da jami'an rundunar ta NATO; ta hanyar bidiyo game da halin da ake ciki a fagen fama, in ji kakakin kungiyar. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira; da a taimaka wa kasarsa da makamai domin yin rigakafi na hare-hare na makamai masu linzame da Rashake kai musu.