1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ki cinyewa a kudancin Kaduna

Mohammad Nasiru Awal
February 15, 2017

Har yanzu ana fama da zaman dar-dar a wasu sassan na kudancin Kaduna, inda daruruwan rayukan mutane suka salwanta sakamakon rikice-rikice. Sai dai har yanzu babu shiri na bin diddigi da samun masalaha a rikicin.

https://p.dw.com/p/2XbFR

Hanyar mota tsakanin garin Kaduna da Kafanchan kan kasance wayam a kowace safiya. Babu mai bin wannan hanya don radin kanshi saboda yawaitar hadura. Sai dai abu mafi damuwa shi ne tashe-tashen hankula da ake yawaita samu tsakanin makiyaya da manoma, wandanda a watannin baya suka yi sanadin daruruwan rayuka.

Ba wanda zai iya sanin ainihin yawan mutanen da aka kashe, amma majami'ar Katholika ta kiyasta cewa za su kai mutane 800, yayin da 'yan sanda suka ce mutum 204 ne, alkalumman da a cewar Mohammed Bello Tukur lauya kuma janara sakatre na kungiyar makiyayan gargajiya na Afirka wato CORET, shi ya fi zama sahihi. 

Takaddama kan mallakar filaye ita ce kan gaba duba da bunkasar al'umma a Najeriya kuma manoma da makiyaya ke rikici kan filaye da ke kara zama dan gabas. Manoma na zargin shanun makiyaya da lalata musu gonaki, su kuma a nasu bangare makiyayan na nuna fushinsu kan yadda ake gine-gine kan burtali da suka shafe shekaru aru-aru suna amfani da su. Sai dai Kabir Kassim shi ne na'ibin limamin masallacin Jumma'a a Zonkuwa da ya ce ana yada jita-jita wajen rurata wutar rikicin.