1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Birtaniya ta saba ka'idojin Brexit

Binta Aliyu Zurmi LMJ
October 1, 2020

Kungiyar Tarayyar Turai ta fara gudanar da taron koli na kwanaki biyu. Batun dankara Birtaniya a kotu kan batun Brexit, na daga cikin batutuwanda shugabannin kungiyar suka mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/3jIvv
Belgien Brüssel | Pressekonferenz Brexit | Ursula von der Leyen
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der LeyenHoto: Johanna Geron/AP Photo/picture-alliance

Kungiyar Tarayyar Turan wato EU, na nunar da cewa Birtaniyan taki mutunta yarjejeniyar da suka cimma a shekarar da ta gabata, wadda ta kunshi dokokin cinikayya a tsakanin bangarorin biyu. A Larabar da ta gabata ne dai, wa'adin da EU ta dibarwa Birtaniyan na janye kudirin dokar soke wani bangare na yarjejniyar Brexit din ya kawo karshe. Matakin na kungiyar Tarayyar Turan, dai wani abu ne da ke kara jaddada irin tsamin dangantakar da ke tsakaninta da Birtaniyan da a baya ta kasance mamba a cikin gamayyar kasashen na Turai. Dukkanin bangarorin biyu na kokarin cimma matsaya ne a kan batun cinikayya kafin karshen wannan shekarar da muke ciki.

Karin Bayani: Birtaniya na son inganta hulda da Afirka bayan Brexit

A jawabinta shugabar Hukumar ta EU, Ursula von der Leyen ta ce matakin da Birtaniya ke son dauka ya sabawa ka'idoji da ma tanade-tanaden yarjejeniyarda suka cimma a baya.

England | House of Commons | Brexit Debatte | Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris JohnsonHoto: picture-alliance/empics/House of Commons

A ranar Talatar da ta gabata,  majalisar dokokin Birtaniya, ta zartar da daftarin kudirin da Firaministan kasar Boris Johnson ya gabatar mata domin zama doka, duk da turjiyar da 'yan bangaren hamayya suka yi tare ma da wasu daga cikin 'yan jam'iyya mai mulki ta Conservative wadda ke da rinjaye a majalisar. 

Karin Bayani: 'Yan Birtaniya sun fusata da Boris Johnson

Mahukuntan kasashen Turan a Brussels na fargabar idan har kudirin na Birtaniya ya zama doka, to akwai yiwuwar sake mayar da shinge a tsakanin yankin Ireland ta Arewa da ta cikin Birtaniya da kuma Jamhuriyar Ireland da ta kasance mamba a kungiyar EU, wanda hakan zai yi karan tsaye ga yarjejeniyar "Good Friday" da aka cimma a shekara ta 1998.

Karin Bayani: EU da matakan da za a dauka kan Brexit

Baya ga batun Birtaniya, shugabannin na EU sun tabo batun takaddamar da ke tsakanin Turkiyya da kasar Girka da Cyprus, kan batun mallakar wani sashe na Tekun Bahar Rum. A jawabinsa, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nanata muhimmancin bai wa kasashen Girka da Cyprus goyon baya, kasancewarsu mambobi a kungiyar ta EU. A game da rikicin bayan zaben kasar  Belarus kuwa, shugabannin na EU na  kokarin ganin sun kawo karshen cin zarafin da Alexanda Luchashenko da ke ikrarin lashe zaben ke yi wa masu zanga-zanga.