1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta hada kai na matakan da za a dauka game da Brexit

Suleiman Babayo MNA
March 13, 2019

Martani bisa matakin majalisar dokokin Birtaniya na kada kuri'ar rashin samun yarjejeniyar Brexit a karo na biyu. Lamarin da ke zama cikas ga bukatun Firaminista Theresa May wadda ta gabatar da kudurin.

https://p.dw.com/p/3ExNj
Frankreich Brexit l Theresa May trifft sich mit Juncker in Strassburg
Hoto: Reuters/V. Kessler

Wannan kuri'a na zuwa kwanaki kalilan gabanin cikar wa'adin fitar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai, EU, da aka fi sani da Brexit, inda ake kasa da kwanaki 20. Haka ya zama cin fuska ga Firaminista Theresa May ta Birtaniya wadda ta gabatar da kuduri sau biyu amma 'yan majalisar dokokin kasar suna watsi da bukatun.

Pierre Moscovici kwamishinan kula da tattalin arziki na Kungiyar Tarayyar Turai yana ganin 'yan majalisar sun yi watsi da dama ta karshe, duk da cewa kungiyar ta nuna sassauci ga Birtaniya a wurare da dama:

"Akwai sauran damar da ake iya samu. An yi daya an yi biyu. Akwai gagarumin rinjayen kuri'u a majalisar dokoki. Kungiyar Tarayyar Turai ta yi duk abin da za ta iya domin samar da mafita da bayar da tabbaci gami da tabbatar da haka. Akwai wata yarjejeniya da muka amince da ita a makon da ya gabata domin kare matsayin Ireland da kasuwarta ta bai daya. Yanzu lokaci ne da Birtaniya za ta bayyana abin da take bukata, domin ta ayyana abin da ba ta bukata."

Treffen der Eurogruppe in Luxemburg
Pierre Moscovici kwamishinan kula da tattalin arziki na Kungiyar Tarayyar TuraiHoto: Getty Images/AFP/J. Thys

Wani bangare mai muhimmanci na zama kasuwar hannun jari a Birtaniya da Turai gami da sauran wurare, kuma martanin ka iya shafar harkokin rayuwa. Duk da lokaci kalilan ya rage wa'adin fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai wato Brexit, ya cika a karshen wannan wata na Maris, sannan an gaza sanin abin da Birtaniya take bukata, bayan watsi da majalisar dokoki ta yi da bukatu biyu da firaministar ta gabatar, sai dai martanin kasuwar hannun jari ya zama mai karfafa gwiwa.

Haig Bathgate yana jagorantar wata cibiyar zuba jari:

"A gaskiya abun mamaki shi ne babu martani daga kasuwar hannun jari, sai dai ma kudin Birtaniya ya haura na Euro. Abin da haka ke nunawa shi ne ko dai suna sane da yanayin da ake ciki ko kuma sun yi watsi da yanayin. Mai yuwuwa abin da aka gani yanzu ke nan, majalisa za ta kada kluri'a kar a samu yarjejeniyar fita wato Brexit, kuma akwai ganin haka ya fi kyau ga kasuwar hannun jari."

Sannan Bathgate ya kara da cewa akwai kwarin gwiwa kasashen Tarayyar Turai za su kara lokaci ga Birtaniya kuma abin da ma kasuwannin suke fata ke nan. Kana wata dama da Birtaniya take da ita na zama yawan kayayyakin da take saya musamman daga kasashen Turai sun gaza abubuwan da take kai wa kasashen, lamarin da ke janyo kowane bangare ya sake duba bukata daga dayan.