SiyasaAfirka
Za a kawo wa Najeriya rigakafin corona a Janairu
December 17, 2020Talla
Ministan kiwon lafiyar Najeriya ya ce kawo yanzu bai san kamfanin rigakafin da Najeriya za ta kawo kasar ba. Ya ce Najeriya na cikin wata tattaunawa da kamfanonin da suka sarrafa rigakafin coronar a Birtaniya da Rasha, to amma ya ce kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba Najeriya shawarar amfani da rigakafin corona ta wani kamfanin kasar Chaina.
Ministan Lafiyar na Najeriya ya ce babu alamun za su yi amfani da rigakafin da kamfanonin Pfizer/BioNTech suka sarrafa domin kasar ba ta da zarafin samar da yanayi mai tsananin sanyi da rigakafin ke bukata a wurin ajiya.