1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum: Fatan inganta rayuwar yara

Salissou Boukari LMJ
June 29, 2021

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama ta bidiyo, inda ya duba halin da yara kanana suke ciki a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3vlEU
Mali Symbolbild Bildung
Rayuwar yara na tagayyara saboda matsalar tsaro a kasar MaliHoto: picture-alliance/AP Photo/UNICEF/Dicko

Shugabannin kasashe da dama da kuma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar António Guterres dai, na cikin wadanda suka halarci wannan taro. A jawabinsa, shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi karin haske kan halin da yara kanana ke ciki a Jamhuriyar ta Nijar da ma kasashen yankin Sahel, inda ake fama da tashe-tashen hankulla. Ya kara jaddada aniyar kasarsa Nijar ta bayar da gudunmawa wajen ba da kariya ga yara kanana a lokutan yaki, inda ya ce yara na fuskantar kalubale mai yawan gaske sakamakon matsalar yanayi da ke haddasa koma bayan tattalin arziki, wanda kuma annobar coronavirus ta kara dagula al'amura. Tashe-tashen hankulla na yake-yake da ke wakana a fadin duniya na haddasa wahalhwalu ga al'umma, inda mutane sama da miliyan 79 suka bar matsugunnansu a duniya.

Karin Bayani: Kokari warware matsalolin ilimin boko a Nijar

Yara kanana ne dai suka fi dandana kudarsu, abin da ya sanya shugaban na Nijar Bazoum ya yi kira da a samar da duniya mai zaman lafiya da yara za su walwala: "Idan aka dauki yankin Sahel inda ake fama da tashe-tashen hankulla, yawan makarantun da aka rufe saboda wannan rikici ya ninka har sau shida tun daga shekara ta 2017, inda aka rufe makarantu sama da 5000. Hakan ya kawo cikas ga karatun yara kanana sama da dubu 700, tare da haramtawa malaman makarantu sama da dubu 20 yin aikinsu na koyarwa. Nijar na nuna damuwarta musamman kan halin rauni da yara mata ke ciki, sakamkon tashe-tashen hakula. Cikin kasashen da ke fama da rikici, yara mata sun fi samun nakasun ilimi fiye da 'yan uwansu a kasashen da babu rikici."

Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar, na son a inganta tsaro da ilimiHoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ya kuma yi fatan ganin an aiwatar da matakan bayar da kariya ga makarantu: "Dangane da wannan yanayi mai firgitarwa na cin zarafin yara sakamakon yake-yake, Nijar na kira da babbar murya kan daukar matakai na zahiri domin bayar da kariya ga makarantu. Don haka babbar sanarwar da shugabannin kasashe suka yi a taron da kasar Nijar ta jagoranta kan batun bai wa makarantu kariya, na bukatar kulawa ta musamman daga manyan kashen duniya."

Karin Bayani: Ƙokarin magance matsalar tsaro a yankin Sahel

Tuni dai kungiyar nan ta EPAD Nijar da ke fafutukar kare hakin yara kanana, ta bakin shugabanta Sidikou Moussa ta yaba da wannan zama na Majalisar Dinkin Duniyar kan halin da kananan yara ke ciki a yankunan da ake rikici, sai dai sun ce fatansu shi ne a gani a kasa wajan gaggauta daukar matakai daga manyan kasashen duniya. Babban zaman taro na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dikin Duniya, ya gudana ne a karkashin jagorancin shugabar kasar Astoniya Kersti Kaljulaid kuma ya samu halartar Henrietta H. Fore da ke zaman babbar daraktar gudanarwa a Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dikin Duniyar UNICEF.