1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabon tsarin tallafawa ilimin yara mata

Ramatu Garba Baba
January 24, 2020

Dalibai mata da aka dakatar daga makarantun boko duk da suna kaunar ci gaba da iliminsu ne suka taki sa'a bayan wani sabon tsarin da hukumomi suka samar na mayar da su makaranta domin ci gaba da karantunsu.

https://p.dw.com/p/3Wme7
Schule in Niamey
Hoto: DW/A. Mamane Amadou

Binciken ya nuna yadda a gundumar Tasawa da ke cikin jahar Maradi, dalibai 'yan mata masu yawa ne ake fidawa daga makarantun boko alhali suna cikin matukar bukatar cigaba da iliminsu, masarautar garin Tasawa ta assasa wani sabon tsari na mayar da wadannan matan makaranta domin su cigaba da karatunsu.

Bücher Bücherstapel Symbolbild Literaturbetrieb Literatur Verlag
Karancin kayan karatu na daga cikin matsalolin da fannin ilimi ke fuskanta a AfirkaHoto: Fotolia/svedoliver

Sabon tsarin ya dauki nauyin mayar dasu makaranta, bayan sun kwashe wata hudu suna zaune a gidan iyayensu ba  karatu ba aikin yi, Mai martaba sarkin Tasawa  Malam Mansur Kane Mai Gizo shi ne ya assasa wanan tsari  tare da tallafin hukumar  majalisar dinkin duniya mai kula da bunkasa rayuwar mata UNFPA, a wani mataki na tallafama karatun yara mata musaman yaran talakawa wadanda basu da halin biya kudin karatu baya an fitar dasu daga makarantun gwamnati.

Kinderehe in Afrika | Elfenbeinküste
Ilimin yara mata na fuskantar koma baya a akasarin kasashen AfirkaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Kungiyar malaman makaranta ta yaba da tsarin na mai martaba, ta ce abin yabawa ne kuma abin koyi kamar yadda Musa Salay daraktan makaratun sakandary na gundumar Tasawa ya bayana .Dukanin shuganin gundumar Tasawa  sun yi baki guda kuma sun dauki matakai dan cimma burin da tsarin ya sa a gaba.