1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro na karuwa a Najeriya

Muhammad Bello LMJ
May 18, 2020

Kimanin rayuka 1,400 na 'yan Najeriya ne suka salwanta a cikin watanni 4 kacal na shekarar da muke ciki ta 2020, inji wani sabon rahoton bincike na kafar Global Rights. Wannan lamari na faruwa a sassa da dama na kasar.

https://p.dw.com/p/3cQzq
Symbolbild Nigeria Polizei
Matsalar rashin tsaro a Najeriya na ta'azzaraHoto: imago/Xinhua

Kafar ta Global Rights dai ta fara ne da bayyana cewar, wadannan rayuka da suka salwanta ko kusa ba su da nasaba da annobar Coronavirus, face fa kashe-kashe da  ke da alaka da tashe-tashen hankula. Ta kara da cewa wannan ibtila'i ya rutsa da fararen hula 1,141 da kuma jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da 'yan sanda da jami'an tsaron farrar hula wa to Civil Defence da na hana fasa kauri har 275.

Kisan gilla ta hanyoyi

Sigar kashe-kashen dai sun hada da na 'yan bindiga da ke karakaina a sassan arewacin kasar, su kuma afka kauyuka suna yi wa mata fyade su kuma kashe na kashewa tare da yin awon gaba da wasu. Baya ga haka su kan budewa matafiya wuta a kan hanyoyin mota ko da rana ko dare. Sai kuma gararin 'yan kungiyar Boko Haram ko kuma ISWAP.

Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hare-haren ta'addanciHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Abin dai bai tsayaiya nan ba, domin kuwa akwai 'yan kungiyoyin asiri, baya ga rikicin  Fulani makiyaya da manoma da na kabilanci gami da kisan gilla da jami'an tsaro kan yi. A yankin Nija Delta dai, rahoton ya nunar da cewa an kashe mutane 57 a jihar Delta da 25 a Edo sai 24 a Rivers kana an kashe 19 a Bayelsa aka kuma kashe 12 a Cross River. A yankin Yarabawa kuwa jimillar mutane 46 aka halaka yayin da aka aika da mutane 45 barzahu a yankin kabilar Igbo.

Matsala mai tayar da hankali

Ire-iren wadannan kashe-kashen dai, sau tari kan haifar da damuwa a ciki da wajen kasar, inda kungiyoyi kamar kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa  Amnesty International da kotun kasa da kasa mai hukunta masu aikata manyan laifuka ICC, ke nunar da cewa tabarbarewar tsaron na Najeriya ya kai makura. Yayin da wasu 'yan Najeriyar ke ganin kafar ta Global Rights ta yi daidai da ta tabo batun matsalar tsaron, masharhanta na ganin sakamakon binciken da ke nuni da yadda al'amuran tsaro suka lalace, batu ne na rashin ingancin shugabanci a kasar.