Rasha ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Ukraine
December 13, 2024Talla
A kalla jirage marasa matuka 200 ne da kuma makamai masu linzami 93 Rasha ta harba zuwa Ukraine a cewar shugaban kasar, Volodymyr Zelenskyy. Sai dai shugaban ya ce, sun samu nasarar kakkabo makamai 81, daga cikin makamai masu linzamin da Moscow ta harba a yankunan yamma da kudu da kuma gabashin kasar.
Shugaba Zelenskyy ya sake jaddada bukatar samun karin tallafin soji daga kasashe kawayen Kyiv, tare da kara kakaba takumkumai masu tsauri ga Moscow. A share guda, ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kwace iko da yankuna bakwai a gabashin Ukraine a cikin wata guda, yayin da dakarun ke kara kutsawa cikin yankin Donetsk, da ke zama wata cibiya ga dakarun Ukraine.