1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO: Tattauna karin makamai ga Ukraine

May 31, 2024

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO na ci gaba da tattauna yadda za a tsara bayar da karin taimakon makamai ga Ukraine da kuma matakin Amurka na bai wa Ukraine din damar amfani da wasu makamanta kan Rasha.

https://p.dw.com/p/4gWCZ
Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens StoltenbergHoto: Peter David Josek/AFP/Getty Images

A yayin zaman taron kwanaki biyu a Jamhuriyar Czech, ana sa ran sanarwar Shugaba Joe Biden na Amurka na bai wa Ukraine damar amfani da wasu makaman Amurka a kan Rasha ya mamaye zauren taron ministocin harkokin kasashen wajen kungiyar NATO, da kuma karin kunshin tallafin yaki ga kasar da ake sa ran za a amince da shi a taron koli na kungiyar da zai gudana a watan Julin wannan shekarar ta 2024 a birnin Washington. Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yin kira kan a amince wa gwamnatin Kyiv ta yi amfani da makaman da ake aika mata wajen kai samame cikin Rasha.

Karin Bayani: Spain za ta ba wa Ukraine manyan makaman yaki

Ko da yake ana ganin ta yiwu kungiyar NATO ta sanya wasu sharudda kan yadda Ukraine za ta yi amfani da makaman, sai dai babban sakataren kungiyar, Jens Stoltenberg ya ce akwai yiwuwar a dage wasu takunkumai na kai hari kan Rasha yayin da fada ke kara matsowa kusa da iyakar Ukraine.

NATO, jiragen yaki
NATO, jiragen yakiHoto: Alexander Welscher/dpa/picture alliance

"Wannan na daga cikin kokarin shugaban kasar Rasha Vladmir Putin da gwamnatinsa na dakatar da kungiyar NATO daga bai wa Ukraine goyon baya domin ta kare kanta, kuma Kyiv na da damar yin hakan. Muna da 'yancin taimaka wa Ukraine kuma hakan ba shi ne ke nuna cewa NATO na kara rura wutar rikici ba. Wannan al'amari ne tun daga watan Fabarairun 2022 kuma hakan zai ci gaba da kasancewa"

Karin Bayani: Rasha ta karbe iko da wasu garuruwa hudu a Ukraine

A yanzu haka dai, dakarun Ukraine na ci gaba da kokarin ganin sun dakile hare-haren da Moscow ke zafafa kai wa a yankin Kharkiv da ke kusa da iyakar kasar. Wasu kasashe mambobin kungiyar na ganin akwai bukatar yin karatun ta nutsu kan dukannin wani mataki da za a dauka sakamakon fargabar da ake da ita na sake rincabewar rikici. Tun da fari, kasashe irinsu Jamus sun ki bai wa Ukraine din manyan makamai masu linzami masu cin dogon zango, inda ta kuma ki bayyana matsayarta kan Kyiv ta kai hari tsallaken iyakarta. Tuni kasashe irinsu su Sweden suke bayyana sassauci kan amfani da makamansu idan har bai saba wa dokar kasa da kasa ba.

Karin Bayani: Jamus da Faransa da Poland sun tabbatar da shirin taimakon Ukraine

Makaman Jamus ga kasar Ukraine
Makaman Jamus ga kasar UkraineHoto: BildFunkMV/IMAGO

"Ministan harkokin wajen Sweden Tobias Billstrom ya ce dukannin tallafin da Sweden ta bayar ga Ukraine babu wani takunkumi, sai dai kawai wanda ya saba wa dokar kasa da kasa. Amma bayan hakan, ta na da ikon yin amfani da su domin kare kanta. Rasha na kai mata hare-hare ba bisa ka'ida ba, idan ana farmaka, kana da damar da za ka kare kanka."

Sai dai gwamnatin Kremli ta yi barazanar cewa, a jira abun da zai biyo baya idan aka kaddamar da hari a cikin kasarta.