Lambar yabo a ranar 'yancin 'yan jarida
May 3, 2021Talla
Wata 'yar jarida mai binciken kwakwaf da ke tarayyar Najeriya, Tobore Ovuorie, ta ci lambar yabo ta DW kan fadin 'yancin albarkacin baki na wannan shekarar ta 2021.
Tobore Ovuorie, tana cikin 'yan jaridu masu binciken kwakwaf da ma bin diddgi a Najeriya. Burinta shi ne tsage gaskiya da kuma bankado boyayyun al'amura.
A shekarar 2013, Ovuorie ta yi kasadar shiga aikin karuwanci na tsawon watanni bakwai da nufin bankado yadda ake safarar mata domin aikin karuwanci da kuma sayar da sassan jiki bil Adama.
Wannan kasada ta sai da rai da Ovuorie ke yi, shi ne ya janyo hankalin shugaban tashar Deutsche Welle, Peter Limbourg, har ya ba ta kyautar ta wannan shekara.