1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Qatar ta dakatar da shiga tsakani a yakin Gaza

Binta Aliyu Zurmi
November 10, 2024

Ma'aikatar harkokin kashen ketare ta Qatar ta ce sanar da janyewa daga matsayinta na mai sasantawa a tsakanin Isra'ila da Hamas.

https://p.dw.com/p/4mqDy
Katar Doha Außenminister Blinken und Mohammed bin Abdulrahman Al Thani
Hoto: Nathan Howard/Reuters/AP/picture alliance

Qatar wacce ta jima tana tattaunawa da shugabannin kungiyar Hamas da na Isra'ila a kokari na kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, ta ce muddin bangarorin biyu ba da gaske suke yi ba ita bata da sauran wani lokaci.

Tattaunawar da Qatar din da Masar gami da Amurka ke jagoranta ta yi nasarar samar da tsagaita wuta a baya da ma musayar fursunoni da wadanda aka yi garkuwa da su ne sau daya kacal a wataun Nuwamban bara.

Wani jami'in diplomasiyyar Qatar ya ce Qatar a shirye take ta sake komawa matsayinta idan bangarorin biyu suka nuna da gaske suna son a cimma matsaya.

A jiya Asabar ne aka cika kwanaki 400 tun bayan kaddamar da yaki a Gaza, ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce sama da mutane 43,000 ne yakin ya hallaka.