1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKatar

Qatar na fargaba kan Isra'ila game da yarjejeniyar Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
June 4, 2024

Kasar Qatar da ke shiga tsakani a rikicin Hamas da Isra'ila ta ce tana dakon matsaya guda da kasar Isra'ilar za ta dauka dangane da sabon tayin yarjejeniyar tsagaita buda wuta a Gaza

https://p.dw.com/p/4gdKM
Kakakin ma'aikatar harkokin weajen Qatar Majed al-Ansari
Kakakin ma'aikatar harkokin weajen Qatar Majed al-AnsariHoto: Imad Creidi/REUTERS

Da ya ke magana a gaban manema labarai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari, ya ce har yanzu kasar ba ta samu wani tabbaci amincewa da sabuwar yarjejeniyar tsagaita buda wutar ba daga Isra'ila.

Karin bayani :  Firaministan Isra'ila ya ce babu batun tsagaita wuta a Zirin Gaza

inda ya ce "Har yanzu muna jiran matsayar Isra'ila kan shawarwarin da Shugaba Biden ya gabatar, mun ga sanarwar da ta saba wa hakan daga bangaren ministan Isra'ila, wannan kuma ba ya bayar da tabbacin cewa Isra'ila za ta karbi yarjejeniyar sulhun."

Karin bayani :  Gaza: Amurka ta gabatar da sabon shirin tsagaita wuta

Kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ke fafatukar ganin bangarorin biyu da ke batakashi sun kai ga amincewa da dakatar da yaki domin kulla wata yarjejeniyar da za ta kai ga samar da zaman lafiya a yankin Gaza da farmakin Isra'ila ya daidaita.