1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan Afirka na yin nasara a gasar kofin duniya

November 24, 2022

Babu wata kasar Afirka da ta taba tsallakewa zuwa matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya. Tsofaffin 'yan wasan Bundesliga sun bayyana dalilai da abin da ya kamata

https://p.dw.com/p/4Jmti
Hoto: ORF

 

Tun bayan gasar farko a shekarar 1930, kungiyoyin Afirka 13 ne suka halarci wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Uku ne kawai suka kai wasan daf da karshe: Kamaru (1990), Senegal (2002) da Ghana (2010). Babu ko daya daga cikin wadannan kungiyoyin da suka kai matakin wasan kusa da na karshe.

'Yan wasan Afirka suna taka leda sosai a kwallon kafa ta Turai, wasun su ma suna cikin manyan 'yan wasa na duniya na yanzu. To me sa kungiyoyin kwallon kafa kasashe a nahiyar Afirka suka koma baya sosai? Yacine Abdessadki, tsohon dan wasan kasa da kasa ne na kasar Morocco

Yacine Abdessadki na kasar Morokko
Yacine Abdessadki dan asalin MorokkoHoto: dapd

"Gaskiya ne a 'yan shekarun nan an samu karin 'yan wasan Afirka da ke taka rawar gani sosai, suna taka leda a fitattun kungiyoyi kwallon kafa na duniya, suna fafutukar neman kyautar Ballon d'Or, da dai sauransu. Yana kara habaka kwallon kafa a Afirka. Amma sai dai a matakan gaba daya har yanzu akwai wasu dalilai da ke haifar da matsala wajen bunkasa kungiyar kwallon kafa a matakin kasa."

Tsohon dan wasan na club din Freiburg ya yi imanin cewa kungiyoyin kwallon kafa na Afirka sun dogara da hazakar taurarinsu da tare da yin watsi da sauran bangarorin. A al'adance a Afirka ba a damu wasu muhimman abubuwa da suka dade da zama tamkar bangaren rayuwa ba a nahiyar Turai da Kudancin Amirka, musamman ma abubuwan tunani. Ko dan wasan da ya fi kowa kwarewa a duniya, bai san abin da zai yi da kwallon ba a cikin yanayi na damuwa, in ji shi.

Wani al'amari da kungiyoyin kwallon kafa na Afirka a wasu lokutan suka rasa shi ne hangen nesa. A cewar Karim Haggui dan wasan baya na Tunisiya, wanda ya bugawa club din Hannover 96 da wasu kungiyoyi wasa:

Karim Haggui na kasar Tunisiya
Karim Haggui dan asalin TunisiyaHoto: picture alliance / dpa

"Ba za ku iya shiga gasar kwatsam watra rana kuma ku kafa babbar manufa kamar isa wasan kwata fainal ba. Idan kun yi hakan, kun makara. Kwallon kafa na Afirka ba shi da tsare-tsaren ci gaba na dogon lokaci. Dole ne a samar da dabarun horarwa, dole ne a yi aiki wajen inganta matakin wasan kwallon kafa a Afirka, kazalika wajibi ne a  saka hannun jari wajen ilimantar da jami'ayin horar da 'yan wasa."

Wannan ra'ayi nasa dai ya zo daya da na Hans Sarpei. Tsohon dan wasan na Ghana, wanda ya buga wa Club din Wolfsburg tsakanin sauran kungiyoyi wasa:

Hans Sarpei dan asalin Ghana
Hans Sarpei dan asalin GhanaHoto: Christian Schroedter/IMAGO

"Na kuma yi imanin cewa 'yan wasan Afirka ko kasashen Afirka suna da matsin lamba fiye da na Turai, saboda abin da ake tsammani daga kasar ya fi girma, abin farin ciki ne sosai a can. Suna son 'yan wasan su yi nasara. Idan kuma aka yi rashin nasara." Kowane ɗan wasa ya san: 'Ok, ba zan iya komawa kasarmu ba da farko, dole ne in koma Turai".

Kungiyoyin Senegal da Kamaru da Ghana da Tunisiya da kuma Morocco za su fuskanci matsin lamba a bana. A cikin 2018, a karon farko tun shekarar 1982, babu wani dan Afirka da ya samu shiga matakin rukuni. Kuma bai kamata a sake maimaita irin wannan koma bayan ba.