1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Qatar 2020: An hana sayar da giya a filayen wasa

Ahmed Salisu
November 18, 2022

Hukumomi a Qatar sun ce ba za su amince a sayar da barasa ba a filayen wasan kwallon kafa da za a taka leda a lokacin gasar cin kofin duniya da za a fara nan da kwanaki biyun da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4JlMi
Qatar Pressefreiheit
Hoto: KARIM JAAFAR/AFP/Getty Images

Masu aiko da rahatanni suka ce Qatar din ta dauki wannan mataki a yau bayan da a baya kasar ta amince kan a sayar da barasar. To sai dai mahukuntan kasar sun ce sun kebe wasu wurare na musamman da za a sayar da bararsa amma kuma mafi akasarin wanda za su iya shiga manyan baki ne.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta ce ta tattauna da hukumomin Qatar inda aka amince a kebe wasu wurare da 'yan kallon za su iya sayen barasar amma fa bayan an kammala wasanni.

Qatar din dai na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam saboda zargin da ake yi mata na tauye hakkin dan Adam.