1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Paparoma ya nemi afuwar yaran da aka ci zarafinsu a coci

September 28, 2024

Firaministan Belgium Alexander De Croo da Sarki Philippe sun caccaki shugaban katolika na duniya Paparoma Francis kan rufa-rufa da kuma bukatar fitar da wani tsari na wanke cocin daga zargin da ake mata kan cin zarafi.

https://p.dw.com/p/4lBjg
Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ke sanya hannu kan littafin ziyarar baki tare da Sarkin Belgium Philippe da mai dakinsa Sarauniya Mathilde
Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ke sanya hannu kan littafin ziyarar baki tare da Sarkin Belgium Philippe da mai dakinsa Sarauniya MathildeHoto: OLIVIER HOSLET via REUTERS

Firaministan na jawabi ne a daidai lokacin da Paparoma Francis ke ziyarar kwanaki uku a kasar ta Belgium.  Firaminista De Croo ya bukaci Paparoman da ya yi duk mai yiwuwa wajen dawo da martabar mutanen da aka zalinta tare da sanya muradunsu a gaba fiye da bukatun majami'ar.

Karin bayani: Fafaroma ya fara rangadi a nahiyar Asiya 

Masharhanta na kallon kalaman na De Croo kan Paparoma a matsayin cin fuska kuma hakan ya keta tsarin karrama bako da kuma martaba diflomasiyyar kasa da kasa a duk inda Paparoman ke ziyara.

Karin bayani: Vatikan ta yi bankwanan karshe da Paparoma 

A jawabin da ya gabatar a yayin ganawa da wadanda aka ci zarafinsu a Brussels, Paparoma Francis ya yi tir da mummunan al'amarin da ya faru a cocin na cin zarafin kananan yara.