1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Fafaroma ya fara rangadi a nahiyar Asiya

Abdullahi Tanko Bala
September 2, 2024

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya fara rangadin kwanaki 12 zuwa kasashe hudu a kudu maso gabashin Asiya.

https://p.dw.com/p/4kBcV
Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis
Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma FrancisHoto: Matteo Nardone/picture alliance

Paparoman mai shekaru 87 a duniya zai fara yada zango ne a Indonesiya.

Duk da kasancewarta kasa mafi yawan musulmi a duniya, Indonesiya na da Kiristoci miliyan takwas da dubu dari shida mabiya darikar katolika.

Daga nan zai wuce zuwa Papua New Guinea da East Timor da kuma Singapore.