1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabon harin 'yan ta'adda ya yi ajalin mutane 22

January 30, 2024

An halaka fararen hula da dama a wani kauye da ke Yammacin Jamhuriyar Nijar a yayin wani sabon hari da ake zargin mayakan jihadi da kai wa.

https://p.dw.com/p/4botb
Afghanistan | Al Kaida Kämpfer
Hoto: AFP/Getty Images

Fararen hula akalla 22 ne aka kashe a yayin wani hari da ake kyauta zaton mayakan jihadi ne suka kai a wani kauye da ke yankin Tillabery a Yammacin jamhuriyar Nijar a kusa da iyakar kasar da Mali, kamar yadda wasu majiyoyi na yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Jamhuriyar Nijar

Shaidun gani da ido sun ce 'yan ta'addar a kan babura guda 20 masu dauke da mutane biyu-biyu kowannensu sun afkawa kauyen da ake kira Motogatta da kimanin karfe hudu na maraicen ranar Lahadi 28.01.2024 inda suka ringa harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya ajalin mutane 22 ciki har da dogaren sa kai.

Karin bayani: Sojojin Nijar sun halaka 'yan ta'adda a Tillabery

Kauyen na Motogatta dai na a Kudu maso yammacin karamar hukumar Tondikiwindi da ke a nisan kilomita 30 daga garin Ouallam wanda shi kuma ke a tazarar kilomita 100 daga birnin Yammai fadar gwamnati.