1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin Nijar da Burkina Faso

Gazali Abdou Tasawa LMJ
June 2, 2021

An kammala wanin zaman taro a Jamhuriyar Nijar, tsakanin Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasar da kuma takwararta ta kasar Burkina Faso kan inganta kare hakkokin dan Adam a kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3uN0s
Burkina Faso - Anschlag auf Splendid Hotel in Ouagadougou
A kan zargi jami'an tsaro da taka rawa wajen take hakkin dan Adam, saboda rashin tsaroHoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

Makasudin haduwar hukumomin biyu dai shi ne musayar bayanai da nazarin hanyoyin inganta yanayin hakkin dan Adam a cikin kasashen biyu, wanda ya tabarbare a sakamakon hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma fadace-fadacen kabilanci. Takanas ta Kano ne dai tawagar jami'an hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar ta Burkina Faso, ta tashi zuwa Jamhuriyar ta Nijar da nufin tattaunawa da takwarorinsu na Nijar din kan yadda za su rinka musayar bayanan tsarin aiki domin su inganta aikinsu na kare hakkin dan Adam a cikin kasashen nasu.

Karin Bayani: Kiran a sake lale kan matsalar tsaro a Nijar

Wannan dai na zuwa ne, a daidai loakcin da matsalolin tsaro masu nasaba da fadace-fadacen kabilanci da kuma hare-haren 'yan ta'adda suka haifar da babban komabaya a fannin ‘yancin dan Adam a kasashen biyu da ma makobtansu. Batun hanyoyin aiwatar da bincike da hada rahoto dangane da abin da ya shafi take hakkin dan Adam da jami'an tsaro ke yi kan fararan hula a yankunan da suke fada da kungiyoyin 'yan ta'adda, na daga cikin muhimman batutuwan da bangarorin biyu suka tattauna.

Burkina Faso |  Siedlung für Binnenflüchtlinge
Matsalolin tsaro a Nijar da Burkina Faso, na janyo take hakkin dan AdamHoto: Giles Clarke/UNOCHA

Antoinette Pouya Saouadogo kakakin hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar burkina Faso ta yi karin haske ga manema labarai: "Kan batun mai cike da tarnaki na jami'an tsaro, hukumar kare hakkin dan Adam ta Nijar ta yi mana bayani dalla-dalla dangane da hanyoyin da ta bi wajen hada rahoto a kan zargin da ake yi wa jami'an tsaro, na cin zarafin jama'ar da ba su ji ba su gani ba da sunan yaki da ta'addanci. Mun fahimci yadda suka yi amfani da kayan aiki da kuma kwararrun jami'an kiwon lafiya, wanda ya ba su damar hada rahoton bincike da ya kunshi hujjoji masu karfi. Muma muna sa ran aiki da wannan hikima domin aiwatar da namu binciken."

Karin Bayani: Yunkurin tabbatar da tsaro a kasashen Sahel

Tawagar jami'an hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Burkina Fason dai, ta bakin Antoinette Pouya Saouadogo ta yi amfani da wannan dama wajen yi wa takwararta ta Nijar bayani kan yadda ayyukan ta'addanci suka taimaka ga tabarbarewar yanayin hakkin dan Adam a Burkina Fason a shekarun baya-bayan nan. A karshen zaman taron dai, hukumomin kare hakkin dan Adam na kasashen biyu sun sha alawashin yawaita irin wannan haduwa lokaci zuwa lokaci da ma sauran takawarorinsu na kasashe makobta, ta yadda za su hada karfi da karfe wajen inganta yanayin 'yancin dan Adam a kasashen nasu baki daya.