1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Bukatar taimaka wa Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 2, 2022

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wa Nijar a fannin tsaro. Guterres ya yi wannan kiran ne, yayin ziyarar da yake a Nijar din.

https://p.dw.com/p/4AjxJ
Majalisar Dinkin Duniya I António Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Bruce Cotler/ZUMA/picture alliance

Jamhuriyar Nijar din dai, na fama da tarin matsalolin tsaro da na sauyin yanayi da ke ci gaba da yi wa kasar illa. A nasa bangaren yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da António Guterres din, shugaban Jamhuriyar ta Nijar Mohamed Bazoum ya nunar da cewa ta'addanci ya tilasta kasar kara yawan sojoji da kuma ba su horo fiye da a baya da kuma samar musu da sababbin kayan aiki. A cewarsa hakan na lakumewa Nijar makudan kudi a daidai lokacin da matsalolin sauyin yanayi ke ci gaba da yi wa kasar illa. A ranar Laraba ne dai António Guterres zai tashi zuwa yankin Oullam na jihar Tillaberi mai fama da matsalolin tsaro da talauci, domin tattaunawar kai tsaye da al'ummar yankin dangane da halin da suke ciki da kuma taimakon da suke fatan samu daga Majalisar ta Dinkin Duniya.