1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun yi wa Nijar illa

Gazali Abdou Tasawa AMA
August 2, 2021

A Jamhuriyar Nijar ana cigaba da martani kan wani harin ta'addanci a garin Torodi na yankin Tillaberi mai iyaka da Burkina Faso da ya hallaka sojojin kasar da dama.

https://p.dw.com/p/3yRYY
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Ayarin sojojin Nijar kan hanyarsu ta zuwa fagen dagaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Ofishin ministan tsaron kasar Nijar ya tabbatar da afkuwar hari wanda ya rutsa da sojojin gwamnatin kasar ta Nijar. Sanarwar ta ce da misalin karfe 11 na ranar Asabar ne sojojin gwamnatin Nijar na Operation Saki 2 kan hanyarsu ta zuwa kai kayan aiki da na abinci ga takwarorinsu da ke girke a sansanin soja na Boni da ke a garin Torodi, suka fada tarkon wani harin kwantan bauna da 'yan ta’addan suka kai masu a cikin motocinsu. Wasu bayanai sun nunar da cewa maharan sun yi amfani ne da rokoki wajen tarwatsa motocin sojojijin gwamnatin na Nijar, inda nan take da dama suka rigaye mu gidan gaskiya wasunsu kuma suka ji rauni. Sannan wata motar sojojin ta uku wacce ta zo kawo dauki domin kwashe sojojin da suka ji rauni ita ma ta hau wata nakiya wacce ta tashi da ita.

A jumulce dai sanarwar gwamnatin ta ce sojoji 15 suka halaka, wasu bakwai suka jikkata kana wasu guda shida suka bata babu duriyarsu ya zuwa yanzu. Kungiyar ‚yan jarida masu kula da harkokin tsaro a Nijar wato RJPS ta bakin magatakardanta Malam Soule Maje mai lakabin Rejeto ta bayyana bukatar sake nazarin solon yaki a wannan yankin, inda ya ce "Dole ne sai hukumomi sun sake dubara."

Karin Bayani: Sojoji sun dakile harin ta'addanci a Nijar

Symbolbild | Niger Islamistischer Terrorismus
Hukumomin Nijar na addu'o'i wa kaburan sojojin da suka hallakaHoto: Boureima Hama/Getty Images

Tun bayan fatattakar da sojojin Nijar suka yi wa mayakan 'yan ta’adda a ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata  inda suka kashe 40 a wani dauki ba dadi da suka yi a kauyen Chomabangou, mayakan 'yan ta’addan suka zafafa kai hare-hare a yankin tare da yin nasarar kashe mutane, kuma su fice ba tare da sojojin Nijar din sun rutsa da su ba.

A cikin kasa da makonni biyu 'yan ta’addan sun kaddamar da hare-hare guda shida a yankin na Tillabery inda suka halaka fararan hula kimanin 35 da kuma sojoji 15. Kawo yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai wannan hari na garin Torodi, sai dai rundunar tsaron Nijar ta sanar da aikawa da karin sojoji da ma jiragen yaki domin farautar wadannan mahara.