1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magance matsalar tsaro a Jihar Zamfara da ke Najeriya

December 26, 2018

A Najeriya sakamakon tabarbarewar tsaro a jihar Zamfara da ke arewa maso yammaci kasar, Shugaban Muhammadu Buhari ya umarci hafsan sojojin sama da ministan cikin gida su je jihar don ganewa idonsu halin da ake ciki.

https://p.dw.com/p/3AenQ
Nigeria Befreite Geiseln Boko Haram
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Wannan umarni dai na daga cikin matakan da gwamnatin ke ganin za su magance matsalar tsaron da ta dabaibaye jihar ta Zamfara. Air Mashal Sadik da ke zaman hafsan saman sojojin Najeriya wanda dai tuni ya isa jihar tare da fara daukar matakan da suka dace.

Game da kisan gilla da satar mutane da ake ba ji ba gani a jihar ta Zamfara gwamnatin tarayya ta sha alwashin dakile wannan matsala cikin lokaci a cewar ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau. Gwamnatin jihar Zamfara ta yi matukar murna da wannan hobbasa da gwmanatin tarayya ta yi sai dai ta bukaci daukar tsauraran matakai a cewar makadsashin gwamnan jihar kuma kakakin majalisar dokoki Sanusi Garba Rukiji. Gwamnatin tarayya gami da jihar ta Zamfara sun sha daukar matakan kawo karshen wannan kashe-kashe amma hakan ya ci tura.