1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazarin kwanaki 100 na mulkin shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

September 5, 2011

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta kai ga cika kwanakin ta ɗari a bisa gadon sarautar mulki cikin bakin ciki da alhinin tashe tashen hankulan da ke neman zaman ruwan dare a tsakanin sassan ƙasar dabam dabam.

https://p.dw.com/p/12TUP
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya cika kwanaki 100 a wa'adin mulki na biyuHoto: AP

A cikin kiftawar ido da bisimmilla ne dai ya ce lokaci ya zo na gyaran fasali da ma makoma ga ɗaukacin al'ummar tarrayar Najeriya. Bai kuma kai ga ɓata lokaci ba wajen ɗaukar hankalin manyan ƙasashen duniya da shugabannin su suka riƙa tururuwa zuwa fadar gwamnatin ƙasar ta Aso Rock.

To sai dai kuma yana shirin share kwanakinsa ɗari bisa gadon sarautar mulki cikin yanayi na baƙin ciki da ɓacin rai ga shugaba Goodluck Ebele Jonathan da a ranar Litinin yayi bikin cika kwanakinsa ɗari bisa gadon sarautar ƙasar ta Najeriya.

Maimakon tsallen murna da kila ma cika bakin irin ci gaban da ƙasar ta Najeriya ke samu dai, Jonathan ɗin ya share wunin Litinin ne yana sauraren ministocin sa dake zuwa ɗaya bayan ɗaya suna jawabin irin nasarorin da suka kai ga cimmawa a ma'aikatu da ma hukumomin da suke jagoranta a kwanaki ɗarin da suka gabata.

Nasara kuma da daga dukkan alamu shugaban bai shirya bikin ta, balle shaidawa 'yan Najeriya su taya shi murna kanta ba. An dai kai ga kwanakin ɗarin ne a cikin halin baƙin ciki da ɓacin rai a bangaren fadar da yanzu haka ta zura ido tana fuskantar karuwar tashe tashen hankula da ma matsalolin tsaro da ke neman zama rowan dare gama ɗaukacin arewacin kasar ta Najeriya.

Anschlag auf ein UN Büro in Abuja Nigeria
Matsalar tsaro a birnin AbujaHoto: dapd

Kama daga matsalar Boko Haram da ke barazanar tsaida al'amura a Abuja da ma wasu sassan ƙasar ta Najeriya ya zuwa rikicin addinin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa dai daga dukkan alamu rikicin na tsaro na shirin shafe nasarorin diplomasiya da kila tattalin arzikin da gwamnatin ke ikirarin cimmamwa a cikin kwanaki dari na kan mulkin. Senator Lawalli shua'ibu dai na zaman sakataren babbar jam'iyyar adawar ƙasar ta CAN kuma a cewar kwanakin ɗarin na zaman shakaru irin na fari ga ƙasar ta Najeriya.

To sai dai in ta yi baki tan a shirin shiga duhu a bangaren nigeriar da ma al'ummarta milliyan sama da 150 a tunanin yan adawar kasar ta Nigeria, daga dukkan alamu karatun bah aka yake ba a tunanin wasu datawa da ma shugabanin al'umar kasar ta Nigeria. General Jeremiah Timbukt Useni dai na zaman shugaban ƙungiyar dattawan arewacin Nigeria ta ACF kuma a cewar sa rashin adalci ne a ɗorawa shugaba Jonathan laifin rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta yanzu haka. Abun jira a gani dai na zaman ƙoƙarin gwamnatin na kaiwa ga iya warware matsalolin na tsaro da ke neman zama karfen kafa ga gwamnatin da ke tabbatar da banbancin ta tsakanin al'umar ƙasar.

Mawallafi: Ubale Musa/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal