Nakasassu masu sana'o'i a birnin Kano
July 20, 2016A bangaren wani gida da kungiyar ta guragu take haya ne, matasanta ke kera kekuna da take baje kolinsu a harabar gidan. Ibrahim Abubakar wanda sai a shekara mai zuwa zai kammala makarantar sakandare ne yake jagorantar sauran matasa biyar da suka dukafa wajen yin aiki gadan-gadan, ya yi kira ga sauran guragu da su zo su koyi sana'a, saboda tuni wasu daga cikin matasa da suka ci gajiyar horon, suka buda nasu wuraren.
Baya ga kekuna akwai babura na guragu da lilo na wasan yara, wadanda matasan kungiyar nakasassun ke kerewa. A cewar shugaban reshen kungiyar na jihar Kano, Alhaji Aminu Inuwa Tudunwada, koyan darasin rayuwa da ya hanashi firamare ne ya sashi kama sana'a inda shima wasu ke samu ta karkashinsa.
Kungiyar nakasassun da Polio ya gurgunta na kokarin ganin matasanta sun yi karatu tare da kama sana'a. Sai duk da wannan kokari, kungiyar ta koka da rashin samun kwarin gwiwa daga mahukunta da ma sauran jama'a domin inganta wannan masana'anta ta yadda guragu da dama za su amfana.