1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta ba marada kunya a gasar cin kofin Afirka

Abdoulaye Mamane Amadou
January 14, 2024

A yayin da kasar Côte d'Ivoire ta fara gasar cin kofin Afirka da kafar dama, mai horas da 'yan wasan Najeriya ya ce kasar za ta nuna bajinta a gasar cin kofin AFCON

https://p.dw.com/p/4bDYR
Hoto: Reuters/T. Hanai

Mai horas da 'yan wasan Super Eagles na Najeriya Jose Peseiro, ya bayyana cewa, Najeriya za ta nuna bajinta a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana da aka soma a kasar Cote d'Ivore.

Kungiyar Super Eagles ta Najeriya,, za ta yi wasanta na farko da Equatorial Guinea, a gasar ta cin kofin nahiyar Afirka, amma kuma sai dai kungiyar za ta buga wasan ne ba tare da wasu fitattun 'yan wasan gabanta ba, wadanda suka fi shahara wajen zura kwallo guda biyu, Victor Boniface da Sadiq Umar, sakamakon raunin da suka samu.

Kasar Cote d'ivoire mai masaukin baki, ta fara gasar da kafar dama, bayan da ta lallasa takwararta Guinea-Bissau, da ci biyu ba ko daya a jiya a birnin Abidjan.