1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

USAID: Najeriya za ta dauki nauyin ma'aikata

February 17, 2025

A wani abun da ke zaman sabon yunkuri na dogaro da kai ga rayuwa da makoma, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta dauki nauyin ma'aikatan da ke a karkashin Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID.

https://p.dw.com/p/4qbNI
Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Greg Baker/AP Photo/picture alliance

Sama da dalar Amurka miliyan dubu daya, Tarayyar Najeriya ta karba daga Hukumar Raya Kasashe ta Amurka wato USAID domin harkokin kiwon lafiya a shekaru biyu baya. Kafin babu zato ba tsammani wata sabuwar manufar gwamnatin Amurkan ta rushe babban tsarin da ke zaman kashin baya, a cikin harkokin lafiya a Najeriyar a halin yanzu. Tsayar da tallafawa shirin yakar annobar HIV/AIDs ko kuma SIDA da tarin fuka da zazzabin cizon sauro dai, na shirin jefa rayuwar mutane miliyan kusan hudu cikin halin ni 'yasu.

Amurka | Shugaban Kasa | Donald Trump | Dakatar da Tallafi | USAID
Sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald TrumpHoto: Al Drago/ abaca/picture alliance

Akwai dai kimanin mutane miliyan daya da dubu 300 da ke dauke da cutar SIDA, ko bayan dubu 400 da ke tarin fuka. Akwai kuma wasu miliyan kusan biyu da kan yi fama da zazzabin cizon sauro duk shekara, baya ga ma'aikatan jiyya dubu 28 wadanda ke barazanar rasa aiki sakamakon tsayar da tallafin mai tasiri. To sai dai, gwamnatin Najeriyar ta ce za ta ci gaba da biyan albashin daukacin ma'aikatan da ke aikin samar da lafiya cikin shirin USAID din. Farfesa Mohammed Ali Pate dai na zaman ministan lafiyar Najeriyar, kuma ya ce kasar tana shirin sauyawa zuwa ga dogaro da kai ta kowanne fanni.

Amurka | Shugaban Kasa | Donald Trump | Dakatar da Tallafi | USAID
Tambarin Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID da Trump ya dakatar da bai wa kudiHoto: ORLANDO SIERRA/AFP via Getty Images

Wani sabon kasafin kimanin Naira miliyan dubu 300 Abujar ta sanar a cikin makon da ya shude, domin cike gibin ayyukan USAID din. Abun kuma da a cewar Dakta Ado Mohammed da ke zaman tsohon shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko a kasar, ke zaman alamun tashi daga bacci bayan share shekara da shekaru cikin babi-ya-Allah. To sai dai kuma ko bayan shirin na lafiya dai, USAID din da ta fada cikin wata sabuwar takaddamar daukar nauyin ayyuka na ta'adda na zaman ta kan gaba a kokarin sake mayar da yara makaranta da ma neman ingantar harkokin mulki a kasar. Najeriyar dai, na tsakanin dogaro da tallafin kasashe na waje da kuma kara nisa a cikin rikicin matsi na rayuwa