1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta ciwo bashi daga bankin duniya

July 14, 2023

A Najeriya majalisar datawan kasar ta amincewa shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya karbo bashi na dalla milyan $800 daga bankin duniya domin talafa wa ‘yan Najeriyar.

https://p.dw.com/p/4TvMD
Cibiyar bankin duniya a Washington
Cibiyar bankin duniya a WashingtonHoto: DANIEL SLIM/AFP/Getty Images

 Gwamnatin Najeriyar za ta karbo bashin na dalla milyan 800 daga bankin duniya. Buba sabon babi ne dai na wannan gwamnatin da take sabuwa fil a karkashin jagorancin shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu daga inda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta tsaya. Amma me 'yan majalisar suka hango har da na bangaren adawa suka amince da karbo bashin a dai-dai lokacin da ake koke na bashin da ke kan Najeriya ya yi yawa da ya sanya kudin ruwan da take biya ya zama mata kalubale.

Majalisar Najeriya ta amince shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ciwo bashin

Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Tuni dai masana a fanin tattalin arziki na  ci gaban kasa ke bayyana damuwarsu a kan batun ciwo bashi da Najeriyar ke ci gaba da yi, musamman bashi na a ci shiru da ba'a ganin ci gaban da ya dace bayan an karbo shi, sanin illar kudin ruwan da ake biya. A yanzu dai bashin da ke kan Najeriyar ya karu da kashi 14.46. Ofishin kula da bashi na Najeriya ya ce a karshen watan Mayu bashin da ake bin gwamnatin Najeriyar ya kai Naira tirliyan 77. Comrade Isa Tijjani mai fafutukar kare hakin jama'a a Najeriya na mai bayyana cewar: '‘Yan Najeriya dai sun sa ido don gani a kasa wai an ce da kare ana biki a gidansu a kan irin tsare-tsare na saukaka rayuwa da gwamnatin za ta bullo da su a dai-dai lokacin da tsadar kayayyaki musamman na abinci irin su masara da shinkafa ya jefa milyoyin 'yan kasar cikn mawuyacin hali na ‘yan rabanna ka wadata mu.