1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Za a sake bude makarantu

Binta Aliyu Zurmi
October 2, 2020

Rahotanni daga tarayar Najeriya na cewar za a bude makarantun gwamnati daga ranar 12 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki.

https://p.dw.com/p/3jLf9
Eco Africa Sendung Nummer 186 | Nigeria Schule
Hoto: DW

Makarantun da ke karkashin gwamnatocin jihohi da na kudi za su bude ne a duk lokacin da suka shirya, ma'aikatar ilimin kasar ce ta sanar da hakan.

Bude makarantun zai shafi makarantun gwamnati 104. Wannan hukuncin dai na zuwa ne bayan da ministan ilimin kasar Malam Adamu Adamu ya ce tun a farkon watan Satumban da ya gabata ake samun raguwar sabbin kamuwa da cutar covid-19 wacce a dalilinta ne aka rufe makarantun.

An shafe tsawon watanni bakwai makaratu na rufe. Najeriya ta sami asarar rayukan mutane sama da 1,100 a sanadiyar cutar corona yayin da ta harbi sama da mutum 59,000