1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi

Uwais Abubakar Idris
November 24, 2022

A Najeriya an fara ganin haske ga bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu bayan da majalisun dokokin jihohi 21 na kasar suka amince da hakan

https://p.dw.com/p/4K1NK
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dama da mataimakinsa Yemi Osinbajo a hagu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a dama da mataimakinsa Yemi Osinbajo a hagu Hoto: Press Office Yemi Osinbajo

Kaiwa ga wannan mataki dai muhimmin ci gaba ne da ya sanya fara murna ga masu goyon bayan baiwa kananan hukumomin Najeriyar ‘yancin cin gashin kansu sanin irin dauki ba dadi da aka dade ana yi tun shekarar 1999 ya zuwa yanzu. Kwamitin majalisar dattawan Najeriyar mai kula da gyare-gayren da ake son yiwa tsarin mulkin kasar ne ya yi zama na musamman a kan wannan batu domin duba halin da ake ciki. 

Bai wa kananan hukumomin ‘yanci ba zai yiwu ba dole sai an yi wa sashi na 7 sakin layi na 162 na tsarin mulkin 1999 gyara domin tabbatar da gudanar da kanana hukumomin. Wannan batu na ‘yancin bai wa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye da kuma ikon gudanar da harkokin mulki bisa tsarin dimukurdiyya gyara ne da aka dade ana nunawa inda gwamnonin jihohi ke tauye kananan hukumomin ta hanyar asusun hadin gwiwa.

A baya an sha yin wannan yunkuri amma sai a shiga yanayi na rijiya ta bayar da ruwa guga ta hana inda gwamnonin jihohin ke yin kafar ungulu da lamarin.