1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Najeriya ta yi kunnen doki da Equatorial Guinea a AFCON

Suleiman Babayo AMA(MBA)
January 15, 2024

Kasashen Afirka na fafata gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar a Côte d'Ivoire, inda tuni tuni aka fara samun abun mamaki bayan Cape Verde ta doke Ghana 2 da 1, yayin da Najeriya da Equatorial Guinea suak tashi 1 da 1.

https://p.dw.com/p/4bGWB
Gasar cin kofin Afirka AFCON I Wasan Najeriya da Equatorial Guinea
Gasar cin kofin Afirka AFCON I Wasan Najeriya da Equatorial GuineaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Kasashe 24 na nahiyar Afirka sun fara karawa a gasar neman cin kofin nahiyar a kasar Cote d'Ivoire, mai masaukin baki ta doke Guinea Bissau 2 da nema, a yayin da Masar da Mozambik suka tashi 2 da 2, Najeriya da Equatorial Guinea suka tashi 1 da 1.

Tawagar kungiyar wasan kwallon Ghana Black Stars, ta sha mamaki daga 'yan wasan kasar Cape Verde da ci 2-1, a wasar ta bude fagen gasannin cin kofin Afrika AFCON 2024, mai masaukin baki kasar Côte d'Ivoire ta fara wasan da kafar dama, inda ta ci Guinea Bissau 2-1, Masar ta yi kunnen doki da Mozambik 2-2, Gambiya ta sha kashi a hannun Senegal mai riko da kofin da ci 3-0.

Gasar Bundesliga | Kungiyar FC Augsburg da Bayer Leverkusen
Gasar Bundesliga | Kungiyar FC Augsburg da Bayer LeverkusenHoto: Harry Langer/dpa/picture alliance

A wasan Bundesliga na lig da ake gudanarwa a nan Jamus, Bayern 3, Hoffenheim 0, Freiburg 0, Union Berlin 0, Mainz 1, Wolfsburg 1,Cologne 1, Heidenheim 1, Augsburg 0, Leverkusen 1, Darmstadt 0, Dortmund 3, Bochum 1, Bremen 1, Monchengladbach da Stuttgart 3-1.

A gasar Tennis ta Australiya Open da aka fara Novak Djokovic daya daga cikin fitattatun 'yan wasan yana fatan sake nuna kansa ga duniya. Adrian Mannarino (20), na France, da Stan Wawrinka, Switzerland, sun tashi 6-4, 3-6, 5-7, 6-3, 6-0, a yayin da 'yar Jamus Tatjana Maria ta fafata da Camila Osorio ta Colombiaya, wasan ya tashi 7-5, 6-7 (4), 6-4. Ita kuwa 'yar wasar Argentina, Nadia Podoroska, ta kece raini da Tamara Zidansek ta Slovenia, inda aka tashi wasan da ci 6-1, 6-0.