1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 60 da samun 'yancin Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 1, 2020

A ranar daya ga watan Oktobar 1960 ne dai, Najeriyar ta samu 'yancin kanta daga hannun Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya.

https://p.dw.com/p/3jIJm
Cartoon - 60 Jahre Unabhängigkeit Nigeria

Bikin na cika shekaru 60 da samun 'yancin kan dai ya zowa Najeriyar cikin matsaloli masu tarin yawa, kama daga na tsaro da ke zaman ja gaba cikin jerin matsalolin, da tattalion arziki da fatara da yunwa da kuma talauci.

Baya ga wadannan matsaloli ma, akwai batu na rashin haskekn wutar lantarki, wanda hakan ke dakile ci-gaban masana'antu da kuma ke taka rawa wajen matsalar rashin aikin yi musamman ga matasa. Fannin ilimi ma ba a barshi a baya ba wajen fuskantar matsala.

Koda yake za a iya cewa annobar coronavirus da ta addabi duniya, ta taka muhimmiyar rawa ga masassarar tattalin arziki da kuma koma bayan harkar ilimi da kasar ke fuskanta yanzu, sai dai duk da haka masana na ganin ya kamata mahukunta su tashi tsaye domin nemawa kasar mafita mai billewa.