1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta lalata hauren giwaye da dama

January 9, 2024

Gwamnatin Najeriya ta lalata hauren giwa da ya kai nauyin tan 2.5 da kuma kudinsa ya kai kusan naira bilyan 10 kwatankwacin dalar Amurka milyan 11.2, a wani mataki na dakile safarar giwaye a kasar.

https://p.dw.com/p/4b2UD
Hoto: Marc Schmerbeck/Zoonar/picture alliance

Kimanin shekaru 30 ke nan da mafarauta suka addabi giwayen da ke Najeriya, kuma tuni adadin dabbobin  ya ragu matuka daga 1,500 zuwa kasa da 400, sakamakon kashe su da mafarautan ke yi domin su mallaki hauren na giwayen.

Minista a ma'aitakar muhalli ta Najeriya Ishaq Salako, ya shaida cewa gwamnati ta lalata hauren giwayen kuma za ta yi amfani da tokar wajen gina gunkin giwa domin tunawa da mahimmancin giwa wajen muhalli.

Duk da cewa Najeriya ta rattaba hannu a yarjejeniyar kare hakkin dabbobi, kasar ta kasance kan gaba a jerin kasashen da ke kashe dabbobi musamman giwaye da sauran sassan nau'ikan dabbobi zuwa kasashen Asiya.