1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta karrama wasu daga cikin 'ya'yanta

Ubale Musa M. Ahiwa
October 11, 2022

Najeriya ta karrama wasu daruruwan 'ya'yanta da ta ce sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasar. Wasu ma daga cikin wadanda aka karraman dai sun jima da rasuwa.

https://p.dw.com/p/4I3Rt
Shugaba Buhari na mika wa Imam Abdullahi Abubakar lambar girmamawa
Hoto: Ubale Musa/DW

A cikin ka ce na ce da nunin yatsa, Najeriya ta karrama wasu yayanta 447 da ta ce sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasar. Wasu dai sun yi nisa a cikin kabari, wasu kuma an fara nuna alamun mantawa da su a harka ta kasa, wasu kuma har yanzu na ta fafatawa bisa mulki. Sai dai kuma sun taru wajen kaiwa ga samun karramawar hukumomi a kasar.

Daya bayan daya ne shugaban kasar Muhammdu Buhari, ya dauki tsawon awoyi yana mika wa wasu fitattun ‘yan kasar su 447 lambobi na karramar ta kasa. Wannan ne dai karo na farkon fari cikin shekaru bakwai da doriya na gwamnatin ta Buhari, kasar ke saka wa ‘ya’yanta da ta ce sun yi fice a harkoki daban-daban.

Mutane shida ne dai aka bai wa babbar lambar karramawa ta GCON da kuma suka hada da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal da babban alkali na kasar mai shari'a Olukayode Ariowola, da tsohon babban alkali na kasar Ibrahim Tanko Muhammad da shugabar hukumar ciniki ta duniya Ngozi Okonji Eweala, da mataimakiyar sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed da wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Bande.

Shugaba Buhari a lokacin da yake karrama Amina Mohammed
Hoto: Ubale Musa/DW

Mutane 55 ne dai aka bai wa kyauta ta biyu ta CFR a yayin kuma da mutane 64 suka samu kyautar CON sannan OFR ta tashi da mutane 70, a yayin kuma da ‘yan kasar 108 suka samu lambar OON. ‘Yan uwa da abokai na arziki dai sun share tsawon wunin na Talata ana ta Owambe bisa kyautar da ke zama ta ba zata.

A'isha Abba Kyari 'ya ce ga tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin kasar Malam Abba Kyari da kuma ta ce kyautar ta wanke mahaifin nasu. To sai dai kuma in har kyautar na shirin ta wanke mattatu, ga Abbas Umar Masanawa da ke zaman tsohon shugaban hukumar dab'i da buga kudade ta kasar kyautar OON na shirin kara masa kwarin gwiwar hidima.

Ko bayan ma'aikata na gwamnati dai kyautar ta kuma burge masu kasuwa irin su Auwalu Abdullahi Rano mai harka ta man fetur da masu siyasa a kasar. Amma kuma in har gwamnatin kasar tana tunanin burgewa, daga dukkan alamu tana da dogon zango kafin iya burge ‘yan kasar bisa kokari na karrama nata.

Mika kyautar ga wasu mukarrabai na shugaban kasar dai a fadar Injiniya Buba Galadima da ke zaman jigo a adawa, na zaman abun kunya ga shugaban da ke ikirarin neman gyara ga kasar ta Najeriya.