1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta karbi allurar riga-kafin corona

Ramatu Garba Baba
August 1, 2021

Gwamnatin Najeriya ta karbi kusan riga-kafin cutar corona miliyan hudu na kamfanin Moderna wanda gwamnatin Amirka ta samar wa kasar da ke yakar sabon nau'in cutar.

https://p.dw.com/p/3yO9S
Corona Impfstoff Moderna Biontech Pfizer
Hoto: CHRISTOF STACHE AFP via Getty Images

Najeriya ta karbi allurar rigakafin cutar korona na kamfanin Moderna kusan miliyan hudu, an isar da rigakafin kasar a wannan Lahadin daga kasar Amirka, wakilan Majalisar Dinkin Duniya dana UNICEF ne suka karbi kayan rigakafin a madadin gwamnatin Najeriya a Abuja babban birnin tarayya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke tunkarar na'uin Delta na cutar koronar da ke kokarin mayar da hannun agogo baya a yakin da kasar ke yi da cutar ta korona. Mutum sama da dubu biyu cutar ta halaka a Najeriya tun bayan bullarta a yayin da ta kama wasu sama da dubu dari da saba'in duk da cewa ana ganin alkaluman ka iya haura hakan.

Daga cikin al'ummar Najeriya miliyan dari biyu da goma, adadin wadanda aka yi wa allurar rigakafin cutar ba su taka kara sun karya ba a sakamakon karancin allurar da kasar ke fuskanta.