1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta bukaci sojojin Nijar su saki shugaba Bazoum

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 3, 2023

Najeriya ta bukaci sojojin Nijar su saki shugaba Bazoum

https://p.dw.com/p/4Zj0S
Hoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Najeriya ta bukaci sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar da su saki hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum domin tafiya wata kasar, idan har suna son a fara tattauna batun janye takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata.

Karin bayani:ECOWAS: Nazari kan dalilan juyin mulki a Afirka

Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ne ya yi wannan jawabi, yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, a daura da taron sauyin yanayi da ke gudana yanzu haka a Hadaddiyar Daular Larabawa.

A ranar 10 ga wannan wata na Disamba ne jagororin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS za su gudanar da taro na musamman a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, domin tattauna batutuwan da suka shafi juyin mulkin sojoji da yankin ke fama da shi.

Karin bayani:ECOWAS za ta yi taro kan matsalolin juyin mulkin sojoji a yankin

Yanzu haka dai kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da kuma Jamhuriyar Nijar na hannun sojoji, yayin da wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Saliyo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 a makon jiya.