1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasa Buhari ko Atiku a zaben 2019?

Ubale Musa Uwais Abubakar Idris ,YB
November 19, 2018

Kasa da 'yan sa'o'i da fara yakin neman zaben shugaban kasa da 'yan majalisun Najeriya, daga dukkan alamu jam’iyyar APC mai mulkin kasar ba ta shirin kyale a kwace mulki ba, yayin da jam'iyyar PDP ta ce ta shirya.

https://p.dw.com/p/38WBM
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Hoto: Atiku Media Office

Tuni dai jam'iyyar APC mai mullki ta kaddamar da muhimman manufofinta a wajen wani taron 'ya'yan jam'iyyar a fadar gwamnatin kasar da ke a Abuja. Akalla makarantu 10,000 ne dai shugaban kasar ya ce zai gyara a duk shekara har na tsawon shekaru hudu bayan gina sabon layin dogo na kusan na zamani na tsawon kilomita dubu biyu a wani abun da ke zaman alamun karkata ta hankali na masu tsintsiyar da ke neman sake zabe.

APC da ta ce ta gani ta kuma kara ingantawa bayan ceto kasar daga hanya mara kyau dai ta kuma ce za ta kara yawan hasken wutar lantarkin kasar daga Megawatt dubu bakwai ya zuwa dubu 11 a cikin wasu shekaru masu zuwa.

Atiku Nigeria Wahl 2015
Atiku Abubakar dai na zama dan takarar da ke barazana ga masu mulki a NajeriyaHoto: Atiku Media Office

To sai dai kuma APC na fuskantar gagarumi na adawa a banagre na ita kanta jam'iyyar PDP da ma manyan tsofaffin sojoji na kasar da suka game kai suka kuma ce ko Atiku ko kafar katako.

To sai dai kuma a fadar Hadi Sirika da ke zaman minista a gwamnatin kasar ko a mafarki al'ummar tarrayar Najeriya basu da burin mai da jiya zuwa yau.

Atiku Abubakar dai ya sha alwashi na bunkasa harkar zuba jari a fannin mai da rage tallafi da rubanya tattalin arzikin Najeriyar nan da 2025 muddin ya yi nasara a zaben na 2019. Ya ce zuba jarin zai sanya a samar wa mutane miliyan biyu da rabi aiki a tsame akalla mutane miliyan 50 daga cikin talauci.

Sau hudu a jere ne dai Alhaji Atiku Abubakar ke neman shugabancin Najeriya, kuma sai a wannan karon ne ya zama dan takara a jamiyyar PDP. Hankali dai ya karkata kan wadannan 'yan takara biyu duk da cewa akwai wasu da ke neman shugabancin na Najeriya.

 Abun jira a gani dai na zaman yadda take shiri da ta kaya a bangare na masu tsintsiyar da ke fatan dorawar da kuma 'yan lemar da ke fadin ta zo karshe.