1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An amince da sabon farashin wutar lantarki a Najeriya

November 2, 2020

Bayan share tsawon kusan wata biyu ana tattaunawa, gwamnatin Najeriya da kungiyoyin kodagon kasar sun kai ga amincewa bisa sabon farashi na wutar lantarki da kimanin kaso 50 cikin 100.

https://p.dw.com/p/3kmVj
Elektrizität Afrika
Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Sabon karin da ke da ruwa da tsaki da kokari na tabbatar da inganta wutar lantarki a cikin tarayyar Najeriya ya kalli karin da ya kai a tsakanin kaso 10 cikin 100 ya zuwa 50 cikin 100 a wani abin da ke zaman iya kudi iya shagalinka.

Attajiran da ke amfana daga hajar mai tasiri ne dai kuma za su fi biyan farashi mai tsada a yayin kuma da talakawa ke shirin biyan kadan bisa adadin da ke akwai cikin kafin sabon karin.

Najeriya dai na kallon zare tallafi a harkar ta wuta da kara farashin na iya kaiwa ga karin zuba jari na kamfanonin rabon wutar da ke tangal-tangal sakamakon kasa karbar kudin wutar tsakanin al'umma.

Duk da cefanar da kamfanoni 11 da ke sana'ar rabon wutar cikin tarayyar Najeriyar dai kasar ta sake kisan tiriliyan daya da miliyan dubu dari bakwai da nufin tallafa wa kamfanonin rabon wutar da ke fadin suna kirga asara.

Abujar dai ta ce tana ba da tallafin da ya kai Naira miliyan dubu dari a shekara a cikin harkar ta wuta, duk da komawar masana'antar tsari na kasuwa alkali.

A baya kungiyoyin kodagon Najeriya sun sha gudanar da zanga-zangar adawa da karin farashin wutar lantarki
A baya kungiyoyin kodagon Najeriya sun sha gudanar da zanga-zangar adawa da karin farashin wutar lantarkiHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma tsarin da ya zo daidai lokacin da 'yan kasar ke jin tasiri na corana har a kwakwalwa dai daga dukkan alamu na iya kaiwa ga bata rai na da dama maimakon kaiwa ya zuwa buri na wadata ta wutar.

Comrade Kabir Nasir na zaman daya a cikin jiga-jiga na kungiya ta kodagon tarrayar Najeriyar da kuma ya ce akwai bambanci a tsakanin abin da bangarorin suka cimma da kuma abin da gwamnatin kasar ta fara aiwatarwa tun daga wannan mako.

Tarrayar Najeriyar dai na kallon wadata ta wutar a matsayin hanya daya tilo da kasar take iya kaiwa ga goga kafada a cikin babbar kasuwa ta nahiyar Afirka da take shirin ta fara ci tun daga farko na shekarar badi.

A cikin wannan mako ne dai Najeriyar ta fara tsallen murnar dorawa a cikin wutar da take rabawa daga megawatt 4000 al'ada ya zuwa megawatt 5,500, a wani abin da ke nuna alamun karuwa ta masu bukatar ta wuta.