1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a rufe makarantun tsangaya a Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
April 22, 2020

A Najeriya gwamnonin Arewacin kasar sun amince da rufe daruruwan makarantun tsangaya da ke dauke da dubban yara saboda kare yaduwar annobar Coronavirus. 

https://p.dw.com/p/3bH0M
children beggers
Hoto: DW

Gwamnonin sun yanke wannan shawarar ce ganin yadda almajirai ke tattare da hadarin kamuwa da cutar COVID 19.

Za a rufe makarantun sannan za a mayar da yaran ga iyayensu ko kuma jihohin da suka fito, a yayin da yaran da suka kasance marayu za a barsu a jihohin da suke karkashin kulawsar gwamnatin jihar.

Kungiyar hakkin musulmi MURIC ta kiyasta cewa akwai yara almajirai sama da yara miliyan goma a Najeriya.